SUNNONI GUDA (5) BIYAR LOKACIN SAUKAR RUWAN SAMA



SUNNONI GUDA (5) BIYAR LOKACIN SAUKAR RUWAN SAMA

Annabi ﷺ ya koyar da al'ummarsa wasu sunnoni masu tsada guda biyar na aiki da na adduar alokacin saukar ruwan sama,amma mafi yawan mutane suna mantawa da aikata wannan sunnonin lokacin saukar ruwan sama.

*1-Sunna ta Farko*
"Lokacin fara saukar ruwan sama sai kace:
*"اللهم صيباً نافعاً"*
*ALLAHUMMA SAIYIBAN NAFI'AN*

Daga Nana A'isha R.A tana cewa,lallai Manzon Allah ﷺ ya kasance idan ya ga ruwan sama yafara sauka yana cewa;
*(اللهم صيباً نافعاً ALLAHUMMA SAIYIBAN NAFI'AN)*
@رواه البخاري .

*2-Sunnah Ta biyu*
"Lokacin da ruwan sama yake sauka,an so ka fito ruwan ya taɓa jikinka,yin hakan sunna ne"

Daga Anas Dan Malik R.A yana cewa:
"Ruwan sama ya samemu tare da Manzon Allah ﷺ ,sai Manzon Allah ﷺ ya yaye tufarsa har ruwan sama ya taba jikinsa,sai akace,ya Manzon Allah miyasa ka aikata haka?? "Sai yace:
*(Domin bai jima da barin wajan Allah Madaukakin sarki ba)*
@رواه مسلم .

*3-Sunnah ta Ukku*
"Idan ruwan sama ya taru,sunnane ka dauka daga cikinsa dan yin alwala ko wanka"

Imam Nawawy Allah yayi masa Rahama yana cewa:
"Idan ruwan sama ya taru sunnane ka dauka daga cikinsa dan yin wanka da alwala daga cikisa, saboda Hadisin da aka ruwaito daga Manzon Allah ﷺ cewa:
*"Ruwan sama ya taro sai Manzon Allah ﷺ yace:(Ku fita dan daukar ruwan da Allah ya kiraye shi ruwa mai tsarki, dan yin alwala domin godiya ga Allah)*

*4-Sunnah ta Hudu*
"Kayi addua ga Allah madaukakin sarki,ka rokeshi alkhairin duniya da lahira,domin lokacin ruwan sama,lokacin ne na amsa addu'a"

Saboda Hadisin da Manzon Allah ﷺ yake cewa:
*(Addua alokaci guda biyu ba'a mayar da su "Ma'ana karbabbune"lokacin kiran sallah da lokacin saukar ruwan sama)*
@صحيح الجامع

*5-Sunnah ta Biyar*
"Bayan an gama ruwan sama sai kace anyi mana ruwan samane daga falalar Allah da ni'imarsa,kuma kana mai yarda da hakan azuciyarka".

Saboda Hadisin Manzon Allah ﷺ lokacin da akayi ruwan sama da dare sai Manzon Allah ﷺ yace:
*(Allah Madaukakin sarki yace:Bayina sun waye gari akwai masu imani dani da kuma masu imani da taurari,wanda yace ayi mana anyi mana ruwan samane daga falalar Allah da ni'imarsa,to wannan shine yayi imani dani kuma ya kafircewa Taurari,amma wanda yace anyi mana ruwane saboda Tauraro kaza da kaza,to wannan yayi imani da Taurari ya kafircemin)*
@صحيح الجامع

Allah ne mafi sani

Allah ya rayamu akan sunnar Manzon Allah ﷺ har zuwa karshen rayuwarmu.

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss
Post a Comment (0)