SHAIƊAN YANA CIKIN MALA'IKU NE KO ALJANU?
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikumus. da fatan Malam yana lafiya,.shin SHAIƊAN yana cikin jinsin aljanune Ko Mala'iku kuma Dame Allah ya halacci mala'iku?
:
*AMSA*👇
:
Wa'alaykumussalam, to dan'uwa malaman tafsiri sun yi sabani game da haka zuwa maganganu guda biyu:
1. SHAIƊAN yana daga cikin mala'iku, saboda faɗin Allah a cikin suratul Bakara aya ta: 34, "Kuma ka ambata lokacin da muka ce da mala'iku su yiwa Annabi Adam (A.S) sujjada, sai suka yi sujjada, in ban da Iblisa da ya yi girman kai" togace Iblisa daga cikin waɗanda ba su yi sujjada ba, yana nuna cewa yana daga cikin mala'iku.
2. SHAIƊAN Aljani ne, saboda faɗin Allah madaukakin sarki "Kuma ka ambata lokacin da muka ce da mala'iku su yiwa Annabi Adam (A.S) sujjada, sai suka yi sujjada, in ban da Iblisa, wanda ya kasance daga cikin Aljanu "Kahaf aya ta: 50, sai ayar ta bayyana cewa daga aljanu yake.
Zance mafi inganci shi ne SHAIƊAN aljani ne, saboda an halicce shi ne daga wuta, su kuwa mala'iku an halicce su ne daga haske, kamar yadda hadisin Muslim mai lamba ta: (2996) yake nuni zuwa hakan, sannan Shaidan yana da zuriyya, wacce take hayayyafa, mala'iku kuma ba sa haihuwa, wannan sai ya nuna ba daga cikinsu yake ba, Wannan yasa za'a dauki ayar suratul Bakara a matsayin tana nufin yana daga cikinsu ta fuskar zaman tare, amma ba ta fuskar halitta ba, sannan mala'iku ba sa sabawa Allah, shi kuma Iblisa yana sabawa Allah.
Allah ne mafi sani.
Don neman Karin bayani duba: Tafsirin Ibnu-jarir 1/507 da Jami'u lada'if attafsir 1/278.
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177