HUKUNCIN JAM'I NA BIYU A MASALLACIN DA YAKE DA LIMAMI RATIBI



HUKUNCIN JAM'I NA BIYU A MASALLACIN DA YAKE DA LIMAMI RATIBI.
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum malam meye halaccin sabunta wani jam'i a masallaci bayan angama na farko ?
:
*AMSA*👇
:
Wa alaikum assalam, ya halatta a sabunta, hakan kuma Mustahabbi ne.
Annabi (SAW) ya ga wani ya zo bayan an yi Sallah, sai ya ce "Wa zai yiwa wannan Sadaka, ya yi Sallah tare da shi?" kamar yadda Tirmizi ya rawaito a hadisi mai lamba ta (220).

Babu hadisi bayyananne yankakke wanda ya hana maimaita jam'in Sallah a Masallaci.
Annabi (SAW) yana cewa: "Sallar Jam'i ta fi sallar mutum É—aya da daraja (27)", duk nassin da yake gamamme ana barin shi a yadda yake sai in an samu dalilin da ya cire wani abu a cikin shi ko ya rage masa karfi .

Allah ne mafi sani

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING wasu da yawa zasu amfana.
Post a Comment (0)