KAFOFIN SADA ZUMUNTA NA ZAMANI A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI // 10



KAFOFIN SADA ZUMUNTA NA ZAMANI A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI // 10
.
Mawallafi: Sheikh Aliyu Said Gamawa
.
Daga cikin canjin da duniya ta samu akwai ƙirƙiro da hanyoyin sadarwa a tsakanin mutane kai tsaye, nan take kuma ba tare da ƙayyadewa, tacewa ko katsewa ba. Waɗannan kuwa su ne hanyoyin sadarwa da sada zumunta da aka fi sani da 'social media'. Waɗannan hanyoyi suna da yawa, amma mafi shahara daga cikinsu sun haɗa da:
.
1. FACEBOOK: An ƙirƙiri fasahar 'Facebook' ne a matsayin hanyar zamani na sadarwa tsakanin jama'a, a Jami'ar Harvard da ke ƙasar Amurka a cikin watan Fabarairu na shekarar 2004. Wani matashi mai suna Mark Zuckerberg ne ya ƙirƙiro wannan fasaha tare da tallafin wani mai suna Edward Saverin, dukkansu ɗalibai ne a wannan makaranta ta Harvard. Sannu a hankali fasahar facebook ta yaɗu zuwa wasu makarantun da ke ƙasar Amurka, sannan kuma ta tsallaka zuwa ƙasashen Ingila, Australia da New Zealand.
.
An yi ta samun ci gaba wajen ƙara inganta wannan fasaha har zuwa shekarar 2007 a lokacin da aka buɗe ƙofofin facebook ga kowa da kowa a faɗin duniya tare da sauƙaƙa hanyoyin fara mu'amala da wannan kafa. Kaɗan daga cikin damar da fasahar facebook ta samar ga masu mu'amala da ita su ne:
.
a) Tana ba da damar gaiyatar abokan mu'amala daga ko'ina a faɗin duniya ba tare da ƙaidi ba, don musayar bayanai, yaɗa labarai, wallafa ƙasidu da tura hotuna kai tsaye a tsakanin juna.
b) Tana ba da damar keɓanta isar da saƙo ga wasu mutane da ake don keɓancewa ba tare da sauran abokan hulɗa sun gani ba.
.
c) Tana ba da damar tura hotuna da kuma wallafa su kai tsaye, lokacin da abubuwa ke gudana ga mabiya shafukan abokan hulÉ—a.
d) Tana ba da damar wani ya nuna amincewa ko jin faɗinsa ga wani al'amari da aka wallafa ko ma ya isar da wani saƙo ta hanyar amfani da alamomi kawai.
.
2. TWITTER: Hanya ce ta aika taƙaitattun saƙonni ga duniya, musamman don isa kai tsaye ga abokan hulɗan da ake bibiyar juna a ƙarƙashin wannan fasaha. A wajen amfani da wannan hanyar isar da saƙo, mutum zai taƙaita bayanansa ne ga harufa 280 ko ƙasa da haka. Kaɗan daga cikin amfanin hanyar sadarwa ta a 'twitter) akwai:
.
i. Kasancewar fasahar ta yi tanadin samar da bayanai ne a taƙaice, mai amfani da wannan kafa yana tattara muhimman bayanai ne a cikin taƙaitattun kalamai don isar wa ga duniya.
.
ii. Kafar na ba da damar sadarwa da musayar ra'ayi tsakanin rukunin mutane, yara da manya, shugabanni da mabiya, kafofin watsa labarai, makarantu da wuraren aiki.
.
iii. Kafar ta samar da yanayin da za a iya isar da saƙo kai tsaye ga duniya ta hanyar bibiyar juna a tsakanin masu hulɗa. Idan mutum guda ya wallafa saƙo, nan da nan sai bayanan su yi ta yaɗuwa a tsakanin mabiya har saƙon ya isa lungu da saƙon duniya.
.
3. YOUTUBE: An ƙirkiri wannan fasahar ne a shekarar 2005 don musayar hotunan bidiyo a tsakanin mutane. Ana amfani da fasahar nan ne wajen wallafa saƙonni cikin hotunan bidiyo don isar da su ga duniya. Fasahar kuma tana ba da damar isar da saƙonnin maganganu tare da hotuna don yaɗa manufa da bayanai ga duniya.
.
4. WHATSAPP: An ƙirƙiri fasahar WhatsApp ne a shekarar 2009, a lokacin da wasu tsofaffin ma'aikatan Yahoo, watau 'Brain Actor' da 'Ja Koum' suka yi ƙoƙarin samar da kafar aika keɓaɓɓun saƙonni na rubutu, hotuna ko magana tsakanin mutane biyu, ko gungun mutane da suka haɗu wuri ɗaya don samar da dandalin musayar saƙonni a tsakaninsu. Sannu a hankali suka yi ta inganta wannan fasahar har ta mamaye ilahirin duniya acikin sirri a tsakaninsu.
.
Wannan fasahar ta zama hanyar da mutane ke iya isar da keɓaɓɓun saƙonni ga juna ba tare da kowa (bayan su) ya ga abin da saƙonnin ke ƙunshe da su ba. Waɗannan saƙonni kuwa sun haɗa da rubutattun bayanai, hotuna da kuma magana a waya ko ta bidiyo kai tsaye.
.
5. BADOO: Wannan kafar sadarwa ce da ta samar da dandalin ƙulla ƙawance da musayar saƙonni a sigar hira tsakanin mutane. An ƙirƙiri wannan salon sadarwa ne a shekarar 2006 tare da fara ƙaddamar da ita a cikin tsakiyar garin London da ke ƙasar Ingila. Kamar sauran hanyoyin zamani na sada zumunta, ita ma wannan fasaha an faɗaɗa ta zuwa hanyar isar da rubutattun saƙonni, hotuna da bidiyo a tsakanin waɗanda suka ƙulla hulɗar a ƙarƙashin wannan hanya.
.
6. INSTAGRAM: Kafar sadarwa ce da mutane ke amfani da ita wajen musayar hotuna da bidiyo ko a keɓe a tsakanin mutane biyo ko kuma a tsakanin tarin jama'a. An ƙaddamar da wannan fasahar ne tun farko a shekarar 2010, sannan aka ci gaba da inganta ta har zuwa shekarar 2016, don ta yi amfani da inji mai ƙwaƙwalwa da wayoyin hannu cikin sauƙi.
.
WaÉ—annan Æ´an kaÉ—an ne daga cikin sababbin kafofin sada zumunta da ake da su a duniya, domin bayan waÉ—annan kafofin akwai wasu makamantansu irin su: IMO, BLACK BERY, TO-GO, TUNE-IN, SNAPSHOT, GOOGLE+, FLICKER, LINKEDIN da dai sauransu.
.
Sannan a ɓangaren sadarwa kuma akwai fasahar buɗe dandali ko zaure na musamman ta yanar gizo wadda aka fi sani da 'Blogging' don wallafe-wallafe, sharhi, yaɗa manufa da ilmantarwa. Har ila yau kuma akwai wata damar ta buɗe shafi na musamman da ake kira 'Website' a matsayin dandalin da za a riƙa ziyarta don samun cikakkun bayanai na waɗanda suka tanadi shafin, don ingiza manufofinsu a faɗin duniya.
.
Bayan wannan akwai hanyoyin bincike da neman bayanai da wasu manhajoji suka tanada don shiga rumbun ilmi da aka tanada a ƙarƙashin wadannan kafofin sadarwa na zamani. Mafi shahara daga cikinsu kuwa ita ce manhajar Google.

.

Rubutawa:- Shaikh Aliyu sa'id Gamawa
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)