ZAMAN MAJALISA:
:
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
:
*TAMBAYA*❓
:
Mln mijina yakasance bayadawowa Sai cikin dare nikuma hakan Yana cutatar dani, Nagayamai Amman yakasa fahimtata Wai yana majalisa
Mln miye hukuncin majalisa aaddinance.
:
*AMSA*👇
:
MAJALISSA...!!!
Ita Majalissa Wuri ne da Maza suke taruwa Domin Karawa Juna Ilimin Rayuwar Duniya ko na Lahira. Mai kyau da Maras Kyau. Ma'ana Zancen Wuta Ko Aljannah.
Sai dai a Irin wannan zamanin Namu a duniyance Kuma, zantattuka Marasa kyau din ya fi mai kyau yawa a MAJALISSAN Mu.
Wannan ne ma yasa mata da yawa ba sa Son Mazajen su suna zuwa Zaman MAJALISSA. Sabida Wata Fitinar daga MAJALISSA Ake Kunno ta, ta zo ta same ki har Mazauninki.
A MAJALISSA Ne fa zaka ji ance wane MATARSA TA FI KARFINSA, MATARSA TA SHANYE SHI, MATARSA TAFI KOWA A WAJEN SA, MATARSA SAI ABINDA TACE ZA'A YI, MATARSA SAI YADDA TAYI DA SHI, MATARSA KAZA-KAZA-KAZA. Musamman ma Wanda Aka Hango yana Zaman Lafiya da Matarsa. Ba'a ji yana kawo Complain din Matarsa MAJALISSA. Duk wannan suna Faruwa a zaman MAJALISSA.
Wani Namijin kuma da ya ji an hakan. To fa Sabida Gidadanci Ko Rashin Zurfin Tunani, An Zuga Shi kenan. Sai yake ji a Zuciyarsa Ashe Haka mutane Suke Yimasa Irin Wannan Kallon, Matar sa tafi Karfin sa? Ashe daman mutane suna kallo na akan sai yadda mata ta Tayi da Ni. Ashe irin wannan Kallon Mutane Suke Yimin. Anan ne kuma Shaidan Zai Shiga Cikin Wannan Tunane-tunanen Nasa. Shikenan kuma idan ya Shigo gida, Sai Rashin zaman Lafiya da Matarsa. Da Sauransu. Ya Tsokano Chan, ya Tsokano Chan. Wai shi Dan dole sai yayi Rigima da Matarsa ya Korata gida, Domin ya Nunawa Duniya, Shi Matarsa ba ta fi Karfin sa Ba. Inba Allah ya Kiyaye ba, ton daga nan Za'a hana Gidansa Samun zaman Lafiya.
A MAJALISSA ne ake Baiwa Wani Shawara ta Banza. Domin wani baya Iya Boye Surrun Zuciyarsa. Da zarar ya zo MAJALISSA. Anan zai Amayar da duk Abinda yake Cikin Zuciyarsa. Sai kuma ace ga yadda zakayi. Wani lokacin ma, babu Tunani. A haka zai je ya yanke Hukuncin da MAJALISSA ta Umarce shi. Daga baya kuma sai ya zo yana da na sani.
Wallahi Billahi Ina Wata MAJALISSA, Wani bawan Allah ya zo da Complain Na Matarsa, akan ga abinda tayi Masa, Kawai Sakinta Zaiyi. Ake Famfa Shi. Cewar ya Kore ta, yayi mata Kaza da Kaza.
Anan ne fa Na Takarkare Nace da shi, wane, kayi Hakuri. Wannan ba wani Abu bane. An yiwa wani abinda ya fi wannan ma yayi Hakuri. Ka da ka sake ka saki Matarka. Kar ka Koreta. Ana son Namiji da Juriya idan Anyi masa ba Daidai ba. Sai Allah ya taimaka ya dauki bayani na. Amma Wallahi da zai dauki Hukunci Ne maras kyau. Kuma ba Mamaki daga baya ya zo yana Nadama.
A zamanin Magabata. Basa Yin Zaman MAJALISSA, sai wadda za'a Tattauna akan Abinda ya Shafi Addini. Itama sai a cikin Yini, ba da dare ba. Da dare Idan anyi sallar Isha'i, kowa Cikin Iyalinsa yake Tafiya.
A nan baya baya ma, MAJALISSIN Imam Ahmad Ibn Hambal. Ba'a yimasa Zancen Duniya. Sai dai Zancen Lahira. Duk wanda yayi masa zancen Duniya. To ba zai kara zuwa masa Majalisinsa ba har Abada. Sai dai ko idan ka Nemi Alfarmar ka dena zancen Duniya ne. Sai a Baka dama ka ci gaba da Zawa Majalisin sa. Amma dai ba zancej Duniya ba.
A irin wannan zamanin Namu. Idan ka je wata MAJALISSAR ma ba zaka sake komawa ba. Sabida Abinda zaka Tarar na Rashin dacewa.
Wata MAJALISSAR ta Masu Girman Kai ce. Sabida haka idan kai ba mai Girman kai bane Irinsu. Rena ka zasu yi. Daga nan Zaka gane ba Irin Tsarinka bane da da su. Sai ka dena Zuwa. Idan kuma ka ci gaba da zuwa, Kaima Irinsu zaka zama.
Wata MAJALISSAR idan ka je, zaka Tarar yan Duniya ne. In banda zancen Banza babu abinda zaka Tarar Anayi. Idan kar Na gari ne kai. Wannan ma zai hana ka cigaba da Zuwa wannan MAJALISSAR. Idan kuma ka ci gaba da Zuwa, Kaima Irinsu zaka zama.
Wata MAJALISSAR zaka tarar Fasikai ne. Sabida haka idan kai ba Fasiki bane. Ba zaka sake Zuwa wannan MAJALISSAR ba. Idan kuma ka ci gaba da zuwa. Kaima Irinsu zaka zama. Ma'ana Kaima zaka zama Fasiki.
Manzon Allah saw baya da wata MAJALISSA sai ta Sahabbansa. Idan ya fito za'a kwashi Ilimi. Sai kuma ya Koma Gida cikin Iyalinsa.
MAJALISSAR Manzon Allah ﷺ ba irin wannan bace za'a dakko zancen wannan a ajiye na wannan. A kwaso na waccan a ajiye na matar Wancan ko na Mijin Waccan. Manzon Allah ﷺ baya yin haka. Idan ya Zauna a MAJALISSAR sa, Sahabbansa zasu Kewaye Shi. Sai ya dinga Karanta Musu Irin abinda Ubangiji SWT ya Karantar da shi.
Asali ma Manzon Allah ﷺ Ya Kyamaci Yin Shira bayan Sallar Isha'i. Domin Mutum ya samu yayi Barci da Wuri, ba Mamaki ko zai dace ya tashi yayi sallar Dare.
Sannan Manzon Allah ﷺ Yace da wani Sahabinsa. "GIDAN KA YA WADACE KA". Sai Manzon Allah ﷺ ya Umarceshi da zama a gida. Tin daga Lokacin da Manzon Allah ﷺ ya gaya masa haka. Akace baya zama a wani MAJALISSA Sai a gidansa.
Kaɗan daga Sharrin zaman MAJALISSA Shine.
YIN JAYAYYA/MUSU DA WANI. Wanda kuma manzon Allah ﷺ ya hana yin Musu. Harma yana cewa, duk wanda ya bar yin jayayya/Musu Akan wani Abinda yake da gaskiya Akansa. Allah ya Tanadar Masa Gida a Tsakiyar Aljannah.
Sannan Manzon Allah ﷺ Yace Allah yana Fushi da Mutumin da yake da yawan Jayayya/Musu.
WANI LOKACIN, ZAMAN MAJALISSA YANA KAWO GABA A TSAKANIN MUSULMAI. Duk Mutumin da Jayayya ta Hada ku da shi. Wannan jayayyar zata Iya zama Fada da Gaba da kuma Fushi a Tsakanin ku.
WANI LOKACIN, ZAMAN MAJALISSA YANA KAWO HASSADA. Idan Mutum ya zo yana bayar da Labarin irin Ni'imar da Allah yayi masa na ci gaba a Rayuwar sa, ko irin kuɗin da yake samu a kasuwarsa ko wani Abu na daban. Sai kaga Wasu daga cikin Mutanen da yake Baiwa wannan Labarin. Da Zaka Bude, Zukatan Wasu daga Cikinsu. Ba daɗin labarin suke ji ba. Sabida ya samu wani abinda su basu Samu ba.
WANI LOKACIN, ZAMAN MAJALISSA YANA KAWO GULMA. DA YADA SURRUN WANI. Manzon Allah saw Yace Duk wanda ka ci Fuskarsa ko ka ci Mutuncinsa ko kayi Gulmar Sa, Za'a dakko Ladanka na Sallah Ko na Azumi ko na kyautatawa Iyaye da kayi a nan gidan Duniya, Sai a bashi. Ko kuma a dakko Zunubinsa da ya Aikata a nan gidan Duniya a Dora Maka.
Kaga Kenan wannan Ba Karamin BALA'I bane. Ace Baka Aikata Lefi ba Anan gidan Duniya. Ka guji Aikata wannan Lefin Anan Gidan duniya. Gashi Kuma an kama ka da shi a Ranar Alkiyama. Asali ma sai kaga shine zai kaika ya zuwa ga Gidan Wuta.
ZAMAN MAJALISSA YANA CINYEWA MACE LOKACIN DA TAKE DA SHI A WAJEN MIJINTA. SHIMA MIJIN YA CINYE MASA NASA LOKACIN. Wannan Ne ma yasa mata da yawa basa son zaman MAJALISSA. Sabida suna son samun lokacin ishashshe, domin Tattaunawa da Mazajensu. Amma kuma MAJALISSA ta Cinye Musu wannan Lokacin.
Wani lokacin ma idan Mutum bai fito ba. Har waya MAJALISSA take Yimasa. ☎️WAI KAI YA AKAYI KA JE KA SA TSOHUWAR MATARKA A GABA KA KASA FITOWA. Wai a dole sai MAJALISSA ta Tsofar Maka da Matar da kai kake ji da ita.
WANI LOKACIN A MAJALISSA AKE ZUGA MUTUM YA KARA AURE. Wanda kuma wannan Shine Babban Masifar Matan da suke Gidan Mazajensu. Ba sa son a Karo Musu Kishiya. Kaga kenan dole ne mata zasuyi Adawa da MAJALISSA. Duk da Cewar Shi Aure Alkairi Ne.
Sai dai kuma ta wani bangaren.
MAJALISSA tana Taimakawa wajen Dubiyar Maras Lafiya, ko daukar Dawainiyar dan MAJALISSA idan bashi da Lafiya har zuwa Asibiti da Sauransu. Musamman ma idan mai Karamin Karfi Ne.
MAJALISSA tana shiga Al'amarin duk wanda yake Member Nata ne idan ya shiga halin da ya kamata a Taimaka Masa. Sannan idan an Baiwa Mutum tension a gida. MAJALISSA tana Iya Baka Labarin da zai sauke maka wannan tension din.
Sai dai Ni Ina Bayar da Shawara ga Wanda yake Magidanci. Ba Za'a Ce ba zai Zauna a Wata Majalissa ba. Amma Dan Allah idan Mutum ya Fito, ya kamata ya Koma gida da Wuri. Minti Talatin ko Ashirin ko Goma ya Isheka Ku gaisa da Mutane. Kar Ace Kwana biyu ba'a Ganinka. Ko ba a gaisa da kai ba. Kayi kokari ka Koma Cikin Iyalinka da Wuri. Domin Suma suna da Hakki Akanki. Asalima Sune Suka Fi Kowa Hakki Akanka, ba yan MAJALISSA ba.
Amma wannan zaman da Mutane Suke yi, har su kai karfe sha biyu ko sha daya ko karfe Goma ko tsakiyar dare a waje. kai ba saye ba, ba sayarwa ba. Menene Wannan Din? Gaskiya ba Daidai bane. Ka Koma Cikin Iyalinka.
Musamman ma wanda zai dawo daga kasuwa. Ka tafi Kasuwa Tin da Sassafe ko wurin Aiki tin Sassafe ko ka wuni a kasuwa kana Zirga-zirga, kuma idan ka dawo Gida kayi wanka ka sake Fita MAJALISSA. Ba zaka dawo ba, sai Cikin Dare. Menene Amfanin irin Wannan.? Kai kenan Baka da Hutu. Kuma iyalinka basu da lokacin ka?
Wani Namijin zai tafi yawonsa. Ko zaman MAJALISSA, Wai sai idan dare yayi, matarsa tayi Barci, Wai kuma Anan ne zai ce zai zo ya neme ta. Idan bata Kula shi ba, Sabida bacci ya dauke ta. Sai ya ji Haushi ko kuma wannan ma ya zama Abin fada. Wanda kuma ba Lefinta bane. Kai ne da Lefi.
Ta yaya Mace zata ji dadin Jima'i bayan barci ya dauke ta. Ta yi wajen Awa Ukku Ko Sama da haka tana yin barci. Lokaci daya kazo kace sai ta bude maka Kafafunta.? Ba zai Yiwu ba...
Sabida haka, dan Allah Maza Muna yin Abinda ya dace. Muna Fita Hakkin Wadannan Bayin Allah. Za'a Tambayemu Akansu fa a Ranar Alkiyama...
Wacce irin amsa kake Tsammanin zaka bayar a gaban Allah ta yadda zamanka ya kasance tare da su a nan gidan Duniya.
Allah ya datar da Mu Duniya da Lahira.
Allah Shine Masani.
✍️
ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08137783797
GROUP ADMIN:👇
Mal. Khamis Yusuf
+2348087788208
+2348054836621