SAYYIDUNA MUKARRAMUN ﷺ
Watarana wani balaraben kauye yazo wajen Sayyiduna Aliyu (rta) yace masa "Yakai Sarkin Muminai! Nazo gareka ne ina so ka lissafa mun halayen Manzon Allah ﷺ".
Sai Sayyiduna Aliyu yace masa "Shin ka iya lissafi? "
Yace "Eh kwarai kuwa".
Sai Sayyiduna Aliyu yace "To zaka iya lissafa mun kayan jin dadin rayuwar duniya?".
Balaraben yace "Ai kayan jin dadin duniya suna da yawa. Gaskiya bazan iya lissafasu ba!".
Sayyiduna Aliyu yace dashi "To ka kasa lissafa kayan duniya duk da cewa 'yan Qaleelan ne kamar yadda Allah ya shaida mana acikin Alqur'ani cewa : "KAYAN JIN DADIN DUNIYA QANKANI NE".
To ta yaya zan iya lissafa maka halaye da dabi'un Manzon Allah ﷺ wadanda Allah da kansa ya shaida mana acikin Alqur'ani cewar "HAKIKA KAI (YA RASULALLAHI) KANA BISA WASU DABI'O'I MASU GIRMA".
Yaku 'Yan uwa ku yawaita salati da tasleemi bisa wannan Babban Masoyi, Annabin Annabawa, Zababben Zababbu ﷺ.
Ya Allah yi salati da aminci gareshi da iyalan gidansa da Sahabbansa gwargwadon girman darajarsa awajenka, sau adadin dukkan abinda ke cikin iliminka.
DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (01/08/2021 21/12/1442)