LALLE AKWAI ABIN LURA!
Wata uku (Semester), ko shekara guda (Session) Malami zai yi yana koyar da Ɗalibi, a duk san da aka ce za a fara jarrabawa wannan Ɗalibin ya shiga cikin firgici, damuwa da tsoron abin da za a tambayeshi.
Zaka yi jarrabawa a bayan ƙasa sama da shekara 40, 50, 60, wani har 100+ amma baka tunanin wace amsa zaka bawa mahallinka!
Zaka ga Ɗalibai suna raba dare suna karatu saboda duniya amma wataƙila wani bai taɓa raba dare ba saboda neman Lahira ba.
Ina ma yadda suke karanta littattafansu suna da lokacin da suke karanta Ƙur'ani da Hadisan Ma'aiki kamar haka!
Ranar da aka kafe sakamako wasu suna bakin ciki wasu suna farin ciki. Haka lamarin yake a lahira.
Yana da kyau mu rinka tunawa da Lahirarmu ko Duniyarmu ta yi kyau.