RAYUWA TARE DA AL-ƘUR’ANI

RAYUWA TARE DA AL-ƘUR’ANI



Dukkan wanda ya tozarta al-Ƙur’ani kuma ya bashi baya ya zamto ba shi da alaƙa mai kyau da al-Ƙur’ani, to tabbas al-Ƙur’ani zai zama mai shaida a kansa kuma ɗaya ne daga cikin hanyoyin halaka da shiga azaba, Allah Ta’ala Ya tsare mu.

Allah Ta’ala Ya ce: “Lallai waɗanda suke karanta littafin Allah kuma su ka tsaida salla kuma suka ciyar daga abun da muka azurta su a fili da ɓoye, su na fatan wani kasuwanci wanda babu faɗuwa”. Suratu Faaɗir 29.

Sannan Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, ya ce: “Ku karanta al-Ƙur’ani domin zai zo ranar al-Ƙiyama ya na mai ceto ga ma’abotansa”. Sahih Muslim 804.

AL-ƘUR’ANI MAI CETO NE DA SHAIDA AKAN MA’ABOCINSA

Jabir ɗan Abdullahi, Radhiyallahu anhu, ya ce: Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, ya ce:

“Al-Ƙur’ani mai ceto ne kuma wanda ake baiwa ceto ne sannan mai shaida ne kuma mai gaskiya – a shaidar shi-, duk wanda ya sanya al-Ƙur’ani a gabansa, to zai jagorance shi zuwa Aljanna, haka nan duk wanda ya sanya shi baya gare shi, to zai ja shi zuwa wuta”. Hadisi ne ingantacce wanda Ibn Hibban ya fitar da shi a Sahih ɗinsa 124 sannan Sheikh Muhammad Nasiruddeen Albani ya inganta hadisin a cikin Sahih al-Jami’ 4443.

A wani hadisin na Abdullahi ɗan ‘Amru, Radhiyallahu anhumaa, Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, cewa ya yi: “Za a ce da ma’abocin al-Qur’ani – a ranar al-ƙiyama-: karanta ka hau kuma ka kyautata karatun shi kamar yadda ka ke yi a duniya; domin matsayinka na ƙarshe ita aya ta ƙarshe da za ka karanta”. Imamu Ahmad a Musnad ɗinsa 2/192 da Abu Dawud a Sunan ɗinsa 1464, sannan Sheikh Albani ya intanga shi a Sahih al-Jaami’ 8122.


Dan uwanku a Musulunci:
Umar Shehu Zaria
Post a Comment (0)