TSORON ALLAH
Allah Ta’ala Ya ce: “Lallai wanda suke tsoron Ubangijinsu a ɓoye, su na wata gafara da sakamako mai girma”. Suratul Mulk 12
Daga Abi Huraira, Allah Ta’ala Ya ƙara yarda a gare shi: Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, ya ce: “Duk wanda ya ji tsoron tafiya, to ya yi sammako kuma duk wanda ya yi sammako zai isa masauki. Ku saurara lallai hajar Allah tana da tsada, ku saurara lallai hajar Allah ita ce Aljanna”. Tirmizi ya fitar da hadisin 2450.
Don haka dai tsoron Allah ya na gadar ma bawa da gafara, ba ma haka ba hatta dawwamarmiyan ni’ima tana samuwa, wato Aljannah.
Dan uwanku a Musulunci:
Umar Shehu Zaria