RUBUTACCIYAR WAΖAR UMMINA 2
WaΖa: Ummina 2
MawaΖi: Aminu Ladan Abubakar Alan WaΖa
Ummi ye Ummi Momina
Ummi ye Ummi Momina
Ummi ye Ummi Momina
Ummi ye Ummi Momina
Jallallah kai ne ka ce a bi iyaye
Ummarni ga tajdidi 'ya'ye
Iyaye ba ai yi musu tawaye
Nasiha za na yiwo kaina tsaye
Ya Allah sanya kar ai mun tawaye.
Ummi ye Ummi Momina
Ummi ye Ummi Momina
Rayuwa a duniya abar tsoro ce ummina
Kyakkyawan asali a waiwayi tsatso ummina
Labarin hankali sai a dubi kamala ummina
Labarin nutsuwa a dubi natija ummina
Halayyar Ιan adam naΖaltar hali ummina
Labarin soyayya tana ga iyaye momina.
Ummi ye Ummi Momina
Ummi ye Ummi Momina
Maza share hawaye ki daina kuka ummi momina
Labarin duniya a je ga fatake ummina
Labarin zuciya sai a tambayi fuska ummina
Labarin kududdufi a je ga agwagwa ummina
Ai hulΙar arziΖi da tunanin kirki dangina
Labarin Ζuruciya a je gun yara dangina.
Ummi ye Ummi Momina
Ummi ye Ummi Momina
Farinciki mai sa a yi kuka da hawaye
Farar uwa alfamar renon 'ya'yaye
NishaΙuwa mai sa a ji kukan tsuntsaye
Adon gani ai ado da tagullar hannaye
Farin dare mai sanya zumuΙin angwaye.
Ummi ye Ummi Momina
Ummi ye Ummi Momina
BaΖin hali mai sa a yi bore tawaye
BaΖin ciki sa 'ya'ya mata su yi maye
BaΖar uwa mai sanya takaici da hawaye
BaΖin dare alfarma ce gun kuraye
BaΖin naΙi mai Ιoye kamannin buzaye.
Ummi ye Ummi Momina
Ummi ye Ummi Momina
Maza share hawaye ki daina kuka Ummi momina
Cuta yau gobe cuta ba mutuwa ba momina
Cuta mai waraka ta zamo kaffara momina
Cuta mara magani a cika da sa'ada momina
Kyakkyawan tanadi ke Ζarkon Ζarshe momina
Allah sa a cika da imani da salama momina.
Ummi ye Ummi Momina
Ummi ye Ummi Momina
Burina addu'a gami da biyayya mai haiba
HaΖuri da ki kai da ni ni Aminu ba zan manta ba
Renon da ki kai mana ba zai yiwu a ce mun rama ba
Addu'ar da ki kai mani ba za fa ta faΙi a Ζasa ba
Allah ya biya maki da Ζarkon Ζarshe da na rabba
Maza share hawaye ki daina kuka ba farau ne ba.
Ummi ye Ummi Momina
Ummi ye Ummi Momina
Tsakar dare rigar sanyawar mugwaye
Wutar ciki mai sanya nadama da tsumaye
AzarΙaΙi mai sa katsalandan kai waye
Jirin cida mai sanya kurame waiwaye
Hassada mai kore nagartar kowaye.
Ummi ye Ummi Momina
Ummi ye Ummi Momina
Ragon amo waΖa da Ιabi'ar Ιeraye
Ragon salo waΖe da salon 'yan nanaye
Ragon maza goga mai dukan mataye
Abin gudu malam da Ιabi'un bokaye
Ruwan dare guΙa a gidajen angwaye
Ummi ye Ummi Momina
Ummi ye Ummi Momina
