ADDU'O'IN KARIYA GA YARA.

ADDU'O'IN KARIYA GA YARA.



*TAMBAYA*❓
:
Assalamu Alaikum, dafatan Malam yana lafya?Allah qarawa Malam basira Malam ko akwai abunda za'a taimaka mana wajen kariya wa yaranmu akan yanayin yanxu na maita da aljannu? Ataimaka mana abun yayi yawa xpecially makaranta abun sunyi yawa.
:
*AMSA*👇
:
Wa'alaykumus Salam, Hakika Addinin musulunci babu abinda ya baro sai da ya mana bayanin komai da komai musamman ma kariya daga sharrin shaidanu.
Har Ma An Ruwaito MANZON ALLAH (saww) yana karantawa Sayyidina Hassan da Husaini addu'o'in kari daga duk wani abin qi.
Daga Cikin Abubuwan da Mahaifiya ya kamata ta rika koyawa yaranta shine Fadar A'UZUBILLAHI MINASH SHAITANIR RAJIM da Kuma Fadin BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM a komai da zasuyi kama daga cin abinci jefa abu a wurin zuba shara (Dustbin) da sauransu.
Daga Cikin addu'o'in da Ake so a yiwa yara akwai,
ﺍﻟﻠﮭﻢ ﺍﻟﮭﻤﮭﻢ ﺭﺳﺪﮬﻢ، ﻭﺍﮐﻦ ﮬﻢ ﻣﻦ ﺳﺮ ﺍﻧﻔﺴﮭﻢ .
ALLAHUMMA 'ALHIMHUM RUSHDAHUM WA A'IDHHUM MIN SHARRI ANFUSIHUM.
Da kuma Wannan addu'ar,
ﺍﻟﻠﮭﻢ ﺟﻨﺒﮭﻢ ﻣﻨﮑﺮﺍﺕ ﺍﻻ ﺧﻼﻕ ﮬﻮﺍﺀ، ﻭﺍﻻﮐﻤﺎﻝ، ﻭﺍﻻﺩﻭﺍﺀ .
ALLAHUMMA JANNIBHUM MUNKARATIL AKHLAQI WAL-AHWA'I WAL A'MALI WAL ADWA.
A Rika dafa kawunansu ana yi Musu In Shaa Allahu Allah zai basu kariya.
ALLAH YA TSAREMU DA ZURI'AR MU DUKA.

WALLAHU A'ALAM.

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)