BAYANI GAME DA MAITA



BAYANI GAME DA MAITA
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalam Alaikun. Shine za'a iya min bayani game da maita ?
Kuma akwai hanyan da ake jinyan wannan matsala a musulunce ?
Domin wlh wannan abu ya daure min kai. Sabida masu aikin jiyyan wadanda mayu suka kamasun matsafa ne. Ko kuma dai nace bansan da me suke jinyan ba.
:
*AMSA*👇
:
Wa'alaikumussalam Na farko dai maita ba halitta bace, Tsafi ce.
.
 Abinda aka sani wanda mutane basa rabewa tsakanin kambun baka da maita. shi kambun baka Allah yana halittar mutum dashi, wanda shi kansa baisan ma yana da wannan halaittar ba,
.
misali, idan mai kambun baka ya Aibanta wani abu, to wannan abun sai ya lalace, idan mutun ne yayi masa wata ba'a ko ya tankashi ko yace kai wannan yaron da kyau yake,
.
musamman ma wadanda suke zuwa wajen barka idan an haifi jariri ko jaririya, anfison mutum ya fadi Alkairi, sabida aibanta wannan halittar, dan da nan zai kamu da jinya a rasa kansa, karshe ma sai yaron ya mutu..
.
Wannan Kambun Baka din ana kiransa da suna العين Da larabci.
  Manzon Allah saw yana yiwa hassan da hussaini wannan addu'ar. yace INA NEMA MUKU TSARIN ALLAH DA KOWANNE SHAIDANI DA KOWANNE MAI KAMBUN BAKA.
 .
Sabida haka kambun baka halitta ne, amma maita Tsafi ce, mai tsafi kuma bazai shiga Aljannah ba.
.
Sannan idan kana yin Addu'ah, Allah zai tsareka, musamman idan zaka fita daga gida, wannan Addu'ar da manzon Allah saw ya koyar akan ، او اضل، عن اظلم او اظلم .
wato Allah ya tsareni kar in cutar kar a cutar dani, kar in batar kar a batar dani, insha Allahu ba wanda zai cutar da kai, Allah zai tsareka, koda kuwa mai maita da kambun baka ya aibantaka.
:
Allah ta'ala yasa mudace
:
Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)