AL-AQEEDA AL-ISLAMIYYA
_____
Rubutu (05)
•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•
✿ Yana batar da wanda ya ga dama sai ya wulakantashi/kaskantashi da adalcinsa, ya kuma shiryar da wanda ya ga dama sai ya datar dashi da falalan sa. Duk wani abu mai sauki shi ne ya saukakeshi kamar yadda ya gabata acikin ilmin sa da ikonsa na daga mutum dan wuta ne ko dan Aljannah.
✿ Tsarki ya tabbata agareshi/ ya girmi ace wani abu ya kasance acikin mulkinsa da baya son faruwarsa, ko kuma wani ya wadatu daga barinsa, ko kuma wani ya halicci wani abu, sai dai shi kadai Ubangijin bayi kuma Ubangijin ayyukansu, mai qaddara musu motsinsu da ajalinsu.
✿ Shi ne wanda ya turo musu Manzanni domin ya tabbatar da hujja akansu, kuma ya cika manzanci da gargadi da Annabta da Annabin sa Muhammad sallallahu alaihi wa sallama, ya sanyashi karshen manzanni, mai bushara kuma mai gargadi, mai kira zuwa ga Allah da ikonsa, yana mai haske abun haskakawa.
✿ Ya saukar masa da littafin sa mai hikima, ya fahimtar da mutane Addininsa ta hanyarshi, ya shiryar adalilinsa zuwa hanyar sa madaidaiciya.
مقدمة ابن زيد القيرواني لكتابه الرسالة...
#Zaurenfisabilillah
TELEGRAM:
https://t.me/Fisabilillaaah
FACEBOOK:
https://www.facebook.com/Fisabilillaaah/
29/9/2020
___