HALAYE DA ALLAH DA MANZON SA SUKE SO

HALAYE DA ALLAH DA MANZON SA SUKE SO


Daga Sahabi Anas Ɗan Malik, Manzon Allah (SAW) ya ce, Bin abu sannu sannu daga Allah ne, (wani abu ne da Allah yake so) Amma garaje wannan daga shaiɗan ne, ba wani wanda ya fi karɓan Uzuri kamar Allah, ba wani abinda Allah ya fi so kamar yabo da godiya da kirari gareshi.


Sannan Imam Muslim ya fitar da hadisi daga Abdullahi ÆŠan Abbas Annabi (SAW) yana gaya ma AbdulQais, cewa; "Kana da wasu halaye guda biyu da Allah da Manzon sa suke son su; HAKURI/JURIYA, DA BIN ABU SANNU SANNU." 

Note:
Amma Game da aikin alheri (aikin lahira)kuwa, a guje ake fita. So samu ka riƙa riga kowa. Kada ka/ki zauna ana barin ka a baya..!
Baya ga wannan kuwa rika bin al'amuran duniya komai a sannu sannu a hankali. gaggawa da garage aikin shaiÉ—an ne. 

Zaurenfisabilillah


Post a Comment (0)