KAJI TSORON ALLAH GAME DA MU!.

KAJI TSORON ALLAH GAME DA MU!.
-


"Kaji tsoron Allah game damu, wannan shi ne furucin gaɓɓai ga dukkanin harshen kowane ɗan adam idan ya wayi gari, ba don komai ba sai don gudun cutarwar da harshe zai yi ga gangunan jikin ɗan adam a ranar ƙiyamah"
-
"Haƙiƙa har yanzu mutane da yawa basu fahimci irin illar da harsunansu suke yi ma gangunan jikinsu ba, musamman ta hanyar yi da mutane, zagin mutane da gulmarsu, da furta kalaman batsa, da dukkanin dangoginsu, haƙiƙa duk wanda bai tsaftace furucinsa dasu ba, to haƙiƙa harshensa zai janyo masa magana a ranar ƙiyamah"
-
"An sami ruwaya daga Abu Sa'id al-Khudri, Allah ya ƙara masa yarda yace: lallai Manzon Allah ﷺ, yace: idan ɗan adam ya wayi gari, to dukkanin ilahirin gaɓɓan jikinsa suna (karkata suna masu) gargaɗar harshensa, suna cewa: kaji tsoron Allah game damu, domin haƙiƙa muma wani sashinka ne, idan ka tsayu to lallai muma mun tsayu, idan kuwa ka karkace to haƙiƙa muma mun karkace"
Jami' at-Tirmidhi : 2407
-

Post a Comment (0)