HANYOYIN TARA KUƊAƊEN GUDANAR DA DA'AWAH DA SAHIHIN TSARIN AMFANI DA SU (1)
*➡️ Muƙaddima [a] ⬅️*
▪️Da'awah ta ƙunshi yin kira zuwa ga imani da Allah, da abin da ManzanninSa suka zo da shi, ta hanyar gaskata abin da suka ba da labari, da yin musu ɗa'a cikin umurninsu.
▪️Kira zuwa ga addinin Allah farilla ce da Allah (Maɗaukaki) Ya ɗora a kan al'ummar Musulmi baki ɗaya.
"Ku ne mafi alherin al'umma waɗanda aka fitar ga mutane, kuna umarni da kyakkyawan aiki, kuma kuna hana mummuna, kuma kuna yin imani da Allah. Da a ce kuwa Ma'abota Littafi za su yi imani da ya fi alheri a gare su. A cikinsu akwai muminai, amma mafiya yawansu fasiƙai ne." Ali Imran, 3: 110
▪️Sai dai kuma tana zama farillar dole a kan shugaba, sannan sai malamai, kasancewar sun ɗauki alƙawari ga Allah (Maɗaukaki) cewa za su bayyana littafinSa, ba tare da ɓoyewa ba. Allah Ta'ala yana faɗa a cikin littafinSa: "(Su ne) waɗanda, idan Muka kafa su a bayan ƙasa sai su tsai da salla su kuma ba da zakka kuma su yi umarni da aikin alheri su kuma yi hani daga mummunan aiki. Ƙarshen al'amari kuwa na Allah ne." Suratul Hajji, 22:41
A wata aya kuma ya faɗa cewa:"Kuma ka tuna lokacin da Allah Ya ɗauki alƙawari daga waɗanda aka bai wa Littafi cewa: "Lallai ku bayyana shi ga mutane, kuma kada ku ɓoye shi." Sai suka jefar da shi can bayansu, kuma suka musanya shi da wani ɗan farashi ƙanƙani. To tir da abin da suke yin musanye da shi." Suratu Ali Imran,3:187
*➡️ Muƙaddima [b] ⬅️*
▪️Ayoyin Alƙur'ani da ingantattun hadisai sun zo da umurni game da yin da'awah.
▪️A cikin Alƙur'ani: "A cikinku lalle a sami wata al'umma waɗanda suke kira zuwa ga alheri, kuma suke umarni da kyakkyawa, kuma suke yin hani daga mummuna. Waɗannan su ne masu rabauta." Ali Imran, 3: 104
A wata aya kuma Ya ce: "Ka yi kira zuwa ga tafarkin Ubangijinka cikin hikima da kyakkyawan wa'azi, ka kuma yi muhawara da su ta hanyar da ta fi kyau. Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sanin wanda ya ɓace daga hanyarsa, kuma Shibnw Mafi sanin shiryayyu." Nahli, 16:125
A wata aya kuma Ya ce: "Muminai maza da muminai mata kuwa masoyan juna ne; Suna yin umurni da alheri suna kuma hana mummunan aiki suna tsai da salla suna ba da zakka suna kuma bin Allah da Manzonsa. Waɗannan Allah zai yi musu rahama. Lalle Allah kuwa Mabuwayi ne Mai hikima." Tauba,9:71
A wata ayar kuma Ya ce: "Ka ce:
"Wannan ce hanyata, ina yin kira zuwa ga Allah, bisa hujja, ni da wanda ya bi ni. Tsarki kuma ya tabbata ga Allah, ni kuwa ba na cikin masu shirka." Yusuf, 12:108
▪️A cikin Hadisai: "Duk wanda ya ga mummuna aiki daga cikinku, to ya kawar da hannunsa, idan ba zai iya ba ya yi da harshensa, idan ba zai iya ba ya ƙi a zuciyarsa; wannan kuma shi ne mafi raunin imani." Muslim
A wani hadisin: "Na ratse da wanda raina ke hannunsa, lallai ku yi umurni da kyakkyawan aiki, kuma ku yi hana ga mummunan aiki, ko kuma ya yi kusa Allah ya aiko muku da azaba daga gareshi, sannan ku yi ta roƙonsa, ba zai amsa muku ba." a
Imamu At- Tirmizi
A wani hadisi kuma ya ce:" Ku isar da saƙona koda da aya ɗaya ce." Bukhari
*➡️ Muƙaddima [c] ⬅️*
▪️Malamai da yawa sun tafi a kan cewa yin kira zuwa ga hanyar Allah da umurni da kyakkyawa da hani da mummuna wajibi ne a kan kowane Musulmi gwargwadon iko.
▪️A tafsirin ayar Ali Imran, 3:104 Ibn Kathir a tafsirinsa, 1/391 ya ce: "Babban abin da ake buƙata shi ne, a samu wasu tawaga wacce za su fuskanci wannan al'amari (da'awah); duk da wajibi a kan ɗaɗɗaikun al'umma."
▪️A ƙarƙashin suratu Yusuf, 12:108, a cikin Fathul Ƙadir, 3/84, Ash-Shaukani ya ce: "(Abin da ake nufi da ni da wanda ya bi ni: Ya yi kira zuwa ga wanda ya bi ni, kuma ya ya bi shiriya ta. Haka kuma a cikin wannan akwai dalili a kan haƙƙi ne a kan dukkanin mabiyin Manzon Allah (S.A.W) ya yi koyi da shi wurin kira zuwa ga Allah; kira zuwa ga Allah da kaɗaita shi, da aiki da abin da ya shar'anta.
*➡️ Muƙaddima [d] ⬅️*
▪️Ana gudanar da ayyukan da'awah saboda dalilai masu yawa:
1) Samun lada mai girma wanda Allah (Maɗaukaki) Ya tanadar wa mai yin da'awah.
2) Yin biyayya da ɗa'a ga umurnin Allah SAW da yin koyi da Annabawa.
3) Samun uzuri wajen Allah (Maɗaukaki) a ranar ƙiyama.
4) Neman tsira da kuɓuta daga fitinar duniya da lahira.
5) Ƙalubalantar ɓarnar maɓarnata da mulhidai, da bayyana wa al'umma gaskiya, da kare martabar sahibin addini, ta yadda mutane za su fahimci gaskiya, kuma su iya bambancewa tsakanin gaskiya da ƙarya.
6) Samar da aminci a cikin al'umma kasancewa da'awah tana sa al'umma ta gyaru kuma al'amarinta ya yi kyau.
*➡️ Muƙaddima [e] ⬅️*
▪️A na gudanar da ayyukan da'awah a kowane lokaci, gwargwadon yanayi da buƙata da kuma iko:
▶️ Dare da rana, kamar yadda Annabi Nuhu As ya yi:
"Ya ce: "Ya Ubangijina, lalle ni na kira mutanena dare da rana." Nuh, 71: 5
▶️ A cikin halin tsanani da ƙunci ko yalwa, kamar yadda Annabi Yusuf As ya yi a cikin kurkuku: "Ya abokaina na kurkuku, yanzu iyayen giji barkatai su suka fi, ko kuwa Allah Ɗaya Mai rinjaye?(*) "Abin da kuke bauta wa wanda ba shi ba, ba komai ba ne face wasu sunaye da ku ka ƙaga ku da iyayenku, waɗanda Allah bai saukar da wata hujja game da su ba. Hukunci na Allah ne kawai; Ya yi umarni cewa kada ku bauta wa kowa sai Shi kaɗai. Wannan shi ne addini miƙaƙƙe, sai dai yawancin mutane ba sa sanin (haka)." Yusuf, 12: 39-40
▶️Hatta a cikin ciwon ajali, kamar yadda Annabi Ya'aƙub AS ya yi ga ga ƴaƴansa: "Ko kuna nan ne lokacin da mutuwa ta zo wa Yaƙubu, lokacin da ya ce wa ƴaƴansa;" Me za ku bauta wa a bayana?" Sai suka ce:" Za mu bauta wa abin bautarka kuma abin bautar iyayenka, Ibrahimu da Isma'ila da Is'haƙa, abin bauta wa guda ɗaya, kuma mu gare Shi muke miƙa wuya." Suratul Baƙara, 2: 133
▶️Haka nan ma, har a lokacin gargarar mutuwa, kamar yadda Manzon Allah SAW ya yi wasiyya game da kiyaye salla da haƙƙoƙin bayi. Imamu Ahmad, Abu Dawud da waninusu suka ruwaito shi.
Sai mun haɗu a rubuta na gaba, in sha Allah za mu ci gaba.
*✍️ Yusuf Lawal Yusuf*
Asalin rubutun maƙala ce da *Ash-Sheikh Prof. Ahmad Bello Dogarawa Hafizahullah,* ya gabatar a taron bita da Majalisar Limamai da Malamai ta jahar Kaduna ta shirya wa mambobinta a ɗakin taro na Jama'atu Nasril Islam, Kaduna, a ranar Litinin 15 ga watan Jumadal Ula, 1443H (20/12/2021).
*20th J. Ula, 1443H (25/12/2021).*