HUKUNCIN CANZA WURI BAYAN SALLAR FARILLA KAFIN SALLAR NAFILA



HUKUNCIN CANZA WURI BAYAN SALLAR FARILLA KAFIN SALLAR NAFILA
:
*TAMBAYA*❓
:
Menene asali ko dalili idan mutum ya idar da salla zai yi nafila sai naga ya ɗan matsa baya ko gaba daga inda yayi sallarsa, akwai hadisi ne akan haka?
:
*AMSA*👇
:
To dan'uwa Akwai hadisin da yake nuna haka, saidai wasu malaman hadisin sun raunana shi kamar Bukhari a sahihinsa, a hadisi mai lamba : 848, amma Albani ya inganta shi saboda yawan hanyoyinsa, a cikin littafin Sahihu sunani abi-dawud 3\178
Saidai malamai suna cewa : ana so ayi hakan saboda gurare da yawa su yi ma mutum shaida,
Amma abin da ya fi ga liman shi ne canza wuri, saboda abin da aka rawaito daga Aliyu - Allah ya kara masa yarda- yana cewa : "Yana daga cikin sunna, liman ya canza wuri idan zai yi sallar nafila" wannan yasa Imamu Ahmad ya karhantawa liman ya yi nafila a inda ya yi sallar farilla, don kar a zaci sallar ba ta kare ba . Fathul-bary 2\335

ALLAH NE MAFI SANI

Dr Jamilu Zarewa 

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)