KHUDUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE:
π 11/JAMADAL-AKHIR/1443-HJRY
π 14/JANUARY/2022-MLDY
π️ GABATARWAππΌAbubakar BN Mustafa Biu
⭕ TOPICππΌ(MAFIYA TSANANIN ASARAR RENIN WAYO GUDA 3️⃣)
➖ mun kasashi gidaππΌ2️⃣
1️⃣ππΌ ASARARRU GUDA 3=
[1] Mutum ne ya mallaki bawa sai yanuna masa 
arbiyyantar dashi tarbiyyar musulunci, bawan uma yayi Ιa'a yabi addini, saidai kash! shi shugabannasa ya saΙawa ALLAH SW bai masa Ιa'a ba,

arbiyyantar dashi tarbiyyar musulunci, bawan uma yayi Ιa'a yabi addini, saidai kash! shi shugabannasa ya saΙawa ALLAH SW bai masa Ιa'a ba,
A ranar Ζiyama sai a shigarda bawan Aljanna, shi kuma shugabannasa a jefashi Wuta, sai yafara ihu wayyo asarana! wayyo baΖin cikina!* ninefa na mallakeshu kuma na mallaki duk abinda yake dashi kuma na tarbiyyantar dashi, meyasa yasami aljanna ni kuma ina wuta⁉️
Sai Mala'ika yace dashi= bawannaka ya tarbiyyantu kai kuma baka tarbiyyantuba, ya kyautata aiki kai kuma ka munana, sai yasami Aljanna kai kuma kafaΙa Wutaπ₯
*[2]* *Mutumne yatara dukiya* ta hanyar saΙon *ALLAH SW* yayi rowansa, ba zakka ba sadaka ba taimako ba neman aljanna dashi, sai magadansa suka gaji dukiyar, sai sukayi sadaka da kyauta da taimako da neman aljanna,
A ranar Ζiyama sai a shigarda magadan Aljanna shikuma da yasha wahalar tara dukiyan a jefashi Wuta! Sai yafara ihu yana cewa *wayyo asarana!* *wayyo baΖin cikina!* ninefa nayi wahalar tara dukiyannan! Meyasa magadana suna Aljanna ni kuma ina wuta⁉️
Sai *Mala'ika* yace dashi= domin su magadannaka sun yiwa *ALLAH SW* Ιa'a kai kuma bakayiba, sunyi sadaka sun ciyar sun nemi Aljanna dashi kai kuma baka yiba, Sai suka sami Aljanna kai kuma kafaΙa Wutaπ₯
_Wandama yafi baΖin ciki da takaici yatara kuΙin kuma bai ciba bai taimaki addiniba sai rowa da Ζowro, sai yamutu matarsa ta gada kuma ta auri wani dabaisha wahalar nemaba yamore matar da kuΙin kuma sutaimaki addini su mutu sushiga aljanna tare shi gogannaka kuma yana wuta!_
*[3]* *Mutum ne ya ilmantarda Mutane yayi musu wa'azi* sai mutane sukayi aiki da iliminnsa da wa'azinnasa shi kuma baiyi aiki dasahiba,
A ranar Ζiyama sai a shigar dasu Aljanna don aiki da iliminnasa shi kuma a jefashi Wuta, sai yafara ihu *wayyo asarana!* *wayyo baΖin cikina!* meyasa waΙannan da ilimina da wa'azina suka shiga Aljanna, ni kuma ina wuta⁉️
Sai *Mala'ika* yace dashi= waΙannan sunyi aikine kyawawa da iliminnaka da wa'azinnaka kai kuma bakayi aiki dashibaπ₯
2️⃣ππΌ *ALHINI*
Yadda kuka sani a rana ita yau juma'a *04/06/1443HJR* ya daceda *07/01/2022MLDY* an jarrabi al'ummar musulmai na Kano da 9jry da ma afirka da ma duniyar musulunci gaba Ιaya- da rasuwar *uba, mai reno, gumi na 2, FADEELATUL SHEIKH AL-MUHADDITH AHMAD IBRAHIM B U K,*
Tabbas al'ummarmu musulmai munyi babban rashin tauraro cikin manyan taurarinmu domin mutuwane na babban faΖihi kuma jajirtacce,
Lallene mutuwar Malamai musibace mai girma wa al'umma da idanu ke kwarararda hawaye akansa, domin mutuwarsu tamkar rufe shafuffukane masu haske na dubban alhairai, tafiyar Malami wagegen giΙine maras toshuwa, kuma rushewane na ginin cigaban mutane, Ιalibai kan tsinci kansu marayun ilimi, tabbas mutuwa doleneππΌ
π‘ *ALLAH SW yace* _"kowace rai zata mutuwa"_ {SRT ANKBT-57}
π‘ *ALLAH SW yace* _"lallene kai mai mutuwane kuma suma zasu mutu_ {SRT ZMR- 30}
Mafi girman rashi mai girgiza zukata shine mutuwar *MALAMAI RABBANIYAI* irinsu *SHEIKH JA'AFAR, SHEIKH ALBANY ZARIA, SHEIKH AHMAD BAMBA* da sauransu, mutuwar WaΙannan zaΖaΖuran jaruman tamkar naΙe shafukane masu haske na alhairai masu yawa a rayuwar Ιaliban ilimi, kuma sun bar wagegen giΙinda bai toshuba,
π³ *SHEIKH AYYUB* yake cewa= duk masu burin mutuwar *Malaman sunnah* suna son dishe hasken *ALLAH SW* ne da bakunansu kuma *ALLAH* mai cika haskensane koda kafirai sunΖi, *[IMAM LALIKA'IY ne yafitar]*
ππ» *YA ALLAH! KAJIΖAN SHEIKH AHMAD BAMBA DA DUKKAN MALAMANMU NA SUNNAH, KUMA KA ALBARKACI WAΖANDA SUKA RAGEN KASA MAKOMA NA KARSHE JANNATUL FIRDAUSI NE*ππ»
*AmiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiNππ»ππ»ππ»*
*viaππΌ Abubakar BN Mustafa Biu [ABU-ABDIRRAHMAN] ✍️*