KO KINSAN HARAMUN NE?

KO KINSAN HARAMUN NE?? 


______________

Sahabi Abdullah bin Ãmir yake cewa: watarana Mamana ta kira ni alhali Manzon Allah yana zaune acikin gidanmu, ta ce: GASHI ZO KA KARBA sai Manzon Allah ya ce Mata "meye zaki bashi"? Sai ta ce: Dabino zan bashi, sai Manzon Allah ya ce mata "Da dai ba wani abu zaki bashi ba (kawai kin fadamasa hakane dan ya zo) to da an rubuta miki ita amatsayin karya (zunubin karya).  
صحيح أبي داود ٤٩٩١

Acikin wannan hadisin zamu fahimci cewa abunda dayawa daga cikin iyaye mata ke fadawa ya'yansu yayin da suke rarrashin su idan suna kuka ko suna so su lallabesu suyi wani abu, kalmomi na karyan za'a basu wani abu ko asaya musu wani abu, ko kuma tsoratar dasu da wani abu, duka wadannan haramunne, hukuncinsa daya da karya. 
عون المعبود ٧/٢٢٧

#Zaurenfisabilillah 

Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah
Post a Comment (0)