YAYA TSARIN ZAMANTAKEWA YAKE WAJEN RABA KWANA TSAKANIN MIJI DA MATANSA, IDAN DAYAN MATAR TAYI TAFIYA TA DAWO?.

YAYA TSARIN ZAMANTAKEWA YAKE WAJEN RABA KWANA TSAKANIN MIJI DA MATANSA, IDAN DAYAN MATAR TAYI TAFIYA TA DAWO?.
:


*TAMBAYA*❓
:
Assalamu Alaikum. Allah yakarawa Malam lafiya, dan Allah tambaya nake. Idan namiji yanada mata 2 sai daya tayi tafiya tayo kwanaki ta dawo, tambayata anan itace ranar da ta dawo wane daki ya kamata mijin ya kwana?
:
*AMSA*👇
:
Wa'alaykumussalam

Mu'amala ta aure da zamantakewa abin da shari'a ke bukata acikin su shine yin adalci, aduk yadda mai gida da iyalansa suka tsara yadda zasu zauna matuka an kiyaye ka'idar (Kada ayi cuta kuma kada a cutar) toh babu laifi, don haka ba laifi don ya shiga dakin wadda tayi tafiya duba ga an dade ba'a haduba. 

*Wallahu A'alam*

*Amsawa*✍🏻
*Malam Nuruddeen Muhammad Mujaheed*
.
Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)