MAFITA {04}

MAFITA {04}


Akwai alamomi mayawaita ga macen da ake kyautata zaton Jinnul Aashiq ne ya shafe ta kamar yadda malamai sukayi bayani, amma ga wasu daga cikin alamomin nan:

1- Yin mafarkin saduwar aure akai-akai da wata fuskar mutumin da kika sani ko wanda baki sanshi ba, kuma yakasance irin fuskar da kika gani a mafarkin jiya itace kuma kika gani ma a yau ko ma kike gani a duk sanda kikayi mafarkin, kuma irin mafarkin nan yawanci za kaga masu komawa bacci ne baya

2- Yawaita mafarkin Jarirai ko na haihuwa ko na shayarwa ko kuma na taron biki ko na aure, kuma yakasance a wurin bikin kina ganin fuskar da kika sani a zahirance wasu ma yan uwanki ne.

3- Yawan jin sha'awa ako da yaushe fiye da misali.

4- Yawan bacci na tsawon awanni.

5- Jin kyamar yin aure da kuma tsanar duk wanda yazo neman aurenki.

6- Jimawa a ban daki (Toilet) wajan yin wanka ko bahaya.

7- Jin kamar ana yin motsi a cikin zaninki, ko kiji kamar wani abu na taba miki gaba, ki duba kiga ba komai.

8- Idan kika kalli wani abu ko da agogon bango ne kuwa sai kiga kamar hoton wani namiji ne a tsirara yana miki gizo.

9- Kuna tare da saurayinki rimi-rimi amma da zarar anyi maganar aure sai kiga lamarin ya lalace, kiga ya kaurace miki ba tare da kunyi a rigima ba, ko kiji ana munana miki wanda za ki aura a haka har ya fita daga rayuwarki. 

10- Son yin soyayya da wani (wanda kinsan ba aure za kuyi ba) tare da yin wasu abubuwan alfasha da shi , da zarar ya bijiro miki da maganar aure kuma shikenan sai kuyi barambaran da shi.

Insha ALLAHu za muci gaba a rubutu nagaba.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani. 

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

Gmail:
rismawy86@gmail.com

WhatsApp :
+2348031542026

Telegram Channel:
https://t.me/Rismawymedicine
Post a Comment (0)