MAFITA {05}

MAFITA {05}


11- Mace tayi ta yawan yin mafarkin an daura mata aure ko ta zama amaryar wasu mutanen da bata san fuskokinsu ba, duk da kuwa a zahirin gaskiya budurwa ce ba ta da aure ko bata taɓa yin aure ba.

12- Mace ta rika mafarkin tana da ciki, ko tana dauke da jariri ko jarirai ko ana mata taron bikin suna ta haihu, alhalin kuma a zahiri ba haka lamarin yake ba.

13- Mace ta rika yin kuka a duk lokacin da wani yazo wajanta neman aurenta, ta yita kawo wasu uzurori waɗanda ko a hankalce ma ba gamsassu bane balle kuma a Addinance, tare da daqile duk wata hanyar da mutumin zai iya dawowa wajan ta.

14- Mace tayi ta kuka haka kurum ba tare da dalili ba.

15- Za kaga mace mai Jinnul Aashiq tana yawan shakuwa da maza barkatai, irin shakuwar nan ta rashin daraja.

16- Akwai wani abu da Malaman Ilimin Maganin musulunci ke kira da ( Hamlu AlKaazib) wato ( Ciki Ko juna-2 na karya), shi ne za kaga mace cikinta ya kumbura ( irin kumburin juna-2 na gaskiya) duk da cewa kuma budurwa ce ita ko an santa da kamewa, aje asibiti a auna amma result din yabada ba juna -2 bane, a haka dai har ta haifar da shi (ta hanyar mafarki ba tare da kowa ya ga jaririn ba), sai kaga a irin yanayin jini ya barke mata ya ki tsayawa. , wannan ma galibi mai irin wannan to sharrin Jinnul Aashiq ne kuma jaririn ma aljani ne,. Allah yakara tsare mu.

Waɗan nan siffofin da na lissafo da ma waɗanda ban lissafo su ba, alamu ne na mace mara aure ta kamu da shafar Jinnul Aashiq, amma ba lallai ne ace dole sai ta hada siffofin gaba daya ba a'a, za ta iya hada wasu kuma yakasance ba ta yin wasu ko kuma wata kaga duk ta hada su gaba daya (Allah ya kyauta).

Tun da mun ji alamun da ake gane shafar Jinnul Aashiq ga mace mara aure, to ya alamun jinnul Aashiq yake ga mace mai Aure ?

Insha ALLAHu a rubutu nagaba za muji yadda lamarin yake.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani. 

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

Gmail:
rismawy86@gmail.com

WhatsApp :
+2348031542026

Telegram Channel:
https://t.me/Rismawymedicine
Post a Comment (0)