MAFITA {07}

MAFITA {07}


8- Idan mijinta na gida ba ta jin sha'awar ya sadu da ita, amma idan baya nan sai taji matsananciyar sha'awa ta lullubeta haka kurum har ta kaita da aikata wani aikin da zai cutar da Addininta, lafiyarta da Kuma mutuncinta kamar Istimna'i ko kallace kallacen batsa da sauransu.

9- Idan cikin mace na yawan barewa kamar a watanni 1 zuwa 6 ko akasin haka, shi ma akwai wanda matsalar jinnul Aashiq ke haifar da hakan.

10- Mace tarika jin wani irin qamshi a dakinta haka kurum ba tare da ta kunna ko wani ya sanya wani turare ba.

11- Mace tayi mafarkin tana kwanciya da wani daga cikin muharramanta kamar Mahaifi ko qani ko kuma yayanta ko danta.

12- Mace tarika neman fitina tsakaninta da mijinta haka kurum, abu kadan wanda bai kai ya kawo ba amma sai ta dauke shi da girma har ta kai tana son a rabu da juna, daga baya kuma tayi ta yin nadamar abinda ta aikata saboda ba a hayyacinta take ba.

13- Mace taji ba ta son mijinta ya kasance ta, ko kuma ta rika jin rashin gamsuwa atare da shi.

Wadan nan Alamomin da ma wasu wanda ban lissafo ba, suna daga cikin alamomin da ake iya gane mace mai Aure tana dauke da Jinnul Aashiq.

Shin mata ne kaɗai ke dauke da Jinnul Aashiq ko kuwa har maza ma suna dauke da Jinnul Aashiq din?

Amsa dai anan kamar yadda malamai masana irin yanayin nan suka bayar shi ne: Namiji ma na kamuwa da Jinnul Aashiq da jinsin mace aljana, kamar yadda itama macen mutun take kamuwa da namijin aljani amma wasu lokutan macen aljani na iya shafar macen mutum ko namijin aljani ya shafi namijin mutum a irin yanayin nan na Aashiq, saboda su ma suna da nau'i na fasiqanci kala-kala kamar yadda mutane ke da shi, kamar 'Yan luwadi da 'yan Madigo, Allah ya kiyaye mu.

Shin tayaya za a gane Jinnul Aashiq yana tare da namiji mai aure ko marar aure?

Insha ALLAHu a rubutu nagaba za muji alamomin cikin iko da yardar Allah..

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani. 

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

Gmail:
rismawy86@gmail.com

WhatsApp :
+2348031542026

Telegram Channel:
https://t.me/Rismawymedicine
Post a Comment (0)