MAHAIFIYATA TA RASU, ANA BIN TA AZUMI!

MAHAIFIYATA TA RASU, ANA BIN TA AZUMI!



:
*TAMBAYA*❓
:
Aslm mlm dan Allah ina da tambaya : tun kafin a kama azumi uwata ba ta da lafiya har akayi sallah, rana ta 16 ga watan karamar sallah Allah yayi mata rasuwa, shin za mu ranka mata azumi ko ba sai mun ranka ba ? Allah ya saka da hairi.
:
*AMSA*👇
:
Wa'alaikumus Salam, To malam mutukar rashin lafiyar ta zarce mata, har zuwa lokacin mutuwarta, to ba za ku rama mata ba, tunda ba sakaci ta yi ba, saboda fadin Allah madaukaki: "Kuma duk wanda yake mara lafiya ko matafiyi to sai ya rama a kwanaki na daban" Bakara aya ta: 185, wato bayan Ramadana, idan mara lafiya ya samu sauki, ko matafiyi ya dawo , Ka ga wanda bai samu sauki ba har ya mutu, zai zama bai kai lokacin da zai rama ba, don haka sai ya saraya akan shi.

Amma idan ta samu damar ramawa, ta yi sakaci ba ta rama ba har ta mutu, to sai makusancinta ya rama mata, saboda faɗin Annabi ﷺ: "Duk wanda ya mutu akwai azumi akansa, to sai makusancinsa ya rama masa". Kamar yadda Bukhari ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta: 1851.

Duba Fataawa nuru aladdarb lamba ta: 247.

Allah Ne Mafi Sani

Dr. Jamilu Zarewa

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)