SAFARAR JAKUNA ZUWA GA ARNA

SAFARAR JAKUNA ZUWA GA ARNA
:


*TAMBAYA*❓
:
Assalamu Alaikum Dr, Barka da dare dafatan kunwuni lafiya Dr. Mutanenmu musulmai suna kaiwa arna jakuna suna ci.
Menene hukuncin dillalai da masu sayarwa da masu saye su kai da direbobin da suke kaiwa da sauran ma'aikata a cikin harkar? 
:
*AMSA*👇
:
Wa'alaikum Assalam, 

A zahirin nassoshin sharia, yin hakan taimakekeniya ne wajan aikata zunubi, Don haka dukkansu sun aikata haramun, tunda Annabi s.a.w. ya haramta cin jakin gida ranar yakin Khaibar.

Siyarwa Wanda aka tabbatar zai ci taimaka masa ne wajan sabawa sharia, wanda ya kiyaye Allah zai kiyaye shi, Wanda ya keta dokokinsa zai same shi a madakata.

*Allah ne mafi sani.*

*Amsawa✍️* 
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)