MENENE FOOTFALLS?

MENENE FOOTFALLS? 
***********************



Footfalls wani lissafi ne da ake bi wajan gano adadi na average ticket da film ya saida. Abinda yasa average ya shigo cikin tsarin shine ticket price yana bambanta a single screen da multiplex, saboda haka se anyi balancing na range dake tsakanin su an maida shi yadda ticket din ze dauki farashi ta hanyar linking nasu. 

Kafin ka san Footfalls se ka san abubuwa guda uku

 1. Ticket price na film
  
 2. Bambancin Ticket price na single screen da multiplex
 
 3. Collection na film

zaka iya amfani da collection na rana guda, ko kuma zaka iya jira se film ya kai lifetime nasa

Next step

Zaka hada ticket price na single screen da multiplex se ka raba shi gida biyu. Kamar haka

SINGLE SCREEN + MULTIPLEX DIVIDED BY 2

Misali idan farashin single screens ya kama N600 Sannan farashin multiplex ya kama N900. Ze zama

600 + 900 = 150

Daga nan se a yi dividing na 150 by 2

150/2 = 750

Next zaka kalli lifetime na film din nawa ya kawo gaba daya 

Idan misali film din ya kawo N5,000 gaba daya collection nasa zaa yi divide by wannan average ticket price din kamar haka 

50000/750 = 66.6 

Ma'ana 66.6 Footfalls 

Hakan na nuni da cewa an saida 66.6 average ticket ko wane ticket guda daya akan average na N750.

750 × 66.6 = 50,000

MU KALLI LISSAFIN YANDA NA HINDI CINEMA YAKE

A Hindi cinema dole se anyi converting. Kasancewar collection na zuwa ne a crore, yayin da ticket da ake siya yana zuwa a rupee

Misali 

Aka saida ticket na single screen a 70 rupees 

Aka saida ticket na multiplex a 100 rupees 

Ze zama 70+100 = 170

170/2 = 85

Average ticket price ya kama 85 rupees kenan 

idan Footfalls na film din duka ake bukata se an jira ya gama kasuwanci an sanar da crore nawa ya kawo officially sannan se ae amfani da wannan collection din. 

Misali idan lifetime na film din ya tsaya a 230 crore, zaayi converting na 230 crore zuwa rupees kamar haka 

1 crore = 10 million rupees 
230cr zai zama 10 million multiplied by 230 = 2,300,000,000 rupees 
Ma'ana 2.3 billion rupees 

Wannan 2.3 billion rupees din zaayi yi divide by average ticket price na film din kamar haka 

2,300,000,000/ 85 = 27,058,823

27,058,823 yana nufin adadin average tickets da aka siyar, ma'ana kowane average ticket yana representing na mutum daya. 

Next zaa yi converting 27,058,823 zuwa crore. Converting nasa zuwa crore na bukatar ayi dividing na 27,058,823 by 10,000,000. 

27,058,823/10,000,000 = 2.7 crore 

Hakan yana nufin cewa 2.7 crore Footfalls aka samu a film din 

Point to note 

Wannan basic ne na kawo, domin harkar Footfalls is very complex, price range yakan samu bambanci daga gari zuwa gari depending on standard of living nasu, koda ace ma screens iri daya ne, 

Lokutan Festivals, holidays, weekends, cinemas sukan kara ticket prices yayin da suke ragewa a ranekun aiki.

A tsakanin cinema da wata cinemar ma zaa iya samun bambanci na ticket price though bambancin ba wani yawa.

#Akk
Post a Comment (0)