SHIN AKWAI ZAKKA A CIKIN ALBASHI ?
*TAMBAYA*❓
:
Malam yaya zakkar ma'aikaci ya kamata ta zamo? Domin wasu ma'aikatu sukan bada alawus a dunkule wanda ya isa zakkah to amma wasu sukanyi gini ko sayen filaye ko gonaki da kudin kafin shekara ta zagayo sun kare.
:
*AMSA*👇
:
To dan'uwa, hukuncin wannan albashi zai fara ne daga lokacin da ya shiga mulkinsa, don haka mutukar ba su shekara ba, to babu zakka a ciki, domin ba kawai samun nisabe ne ya ke wajabta zakka ba, dole sai an samu zagayowar shekara daga lokacin da kudin su ka shiga mulkinsa, don haka duk albashin da ya kai nisabin zakka, kuma aka ajjiye shi ya shekara to ya wajaba a fitar masa da zakka, amma mutukar shekara ba ta zagayo masa ba, to zakka ba ta wajaba ba akan wanda ya mallake shi ba.
saidai yana daga cikin dabarun da sharia ta haramta, mutum ya yi abin da zai sarayar masa da wajibi da gangan, don haka mutukar ya sayi filayan ne da nufin kaucewa fitar da zakka, to tabbas ya sabawa Allah.
Allah ne ma fi sani
JAMILU ZAREWA
Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
WHATSAPP👇
https://wa.me/+2348087788208
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ