WANI ANGO DA AMARYARSA !!!
Wani angone bayan an daura aurensa da kwana biyar, Ya gayyaci abokanansa domin suci abinci a gidansa Ko suma sunyi zuciya suyi aure. Washegari ya gayyacesu, bayan sun karasa gidan suka gaisa da amaryarsa, sannan ya saukesu a palour yaje ya samu matarsa tana kwance a gado. Yace. '' Ina abincin da kika girka mana? Kinsan na fada miki yau zan kawo abokaina suci abincin amarya.
Ta dubeshi a yatsine tace. '' Ni yau banyi komai ba a gidan nan, Sai fa Kunu, don shi nake da sha'awar sha. Angon nan ranshi ya baci, ya rasa me zai ce mata, Kawai ya juya ya tafi ya samu abokanansa ya basu hakuri, Sannan ya kwashesu suka tafi wani Restaurant sukaci abinci suka koshi. Ango fa abin ya dameshi, washe gari zai fita, amarya
tace. '' Mai-gida kudin cefene fa? Yace ayi kunu, gari ya sake wayewa, zai fita, tace mai gida me za'ayi yau ? Yace. '' Kunu.
Akayita jera kuna, shikuma baya sha, Restaurant yake zuwa yana take cikinsa. Amarya taga abin ba dama, Saita dauki mayafinta ta tafi gida. Babanta ya gani yayi tunanin wuni tazo, Yaga har dare bata tafi ba. Ya kira mijin a waya ya tambayeshi lafiya? Mijin ya fada masa komai. Sai uban yace kada yazo, Kuma kada ya nemeta a waya. Gari ya waye, baba zai fita, sai matarshi tace. '' Mai gida me za'ayi yau a gidan ? Yace. '' kunu'', Washe gari haka, akayita jera kunu. Amarya tagafa abin fa yayi yawa wai shege da hauka. Don haka taje ta samu babanta ta gaishe shi. Tace. '' Zata koma gidan mijn ta. Yace. '' Shikenan, Allah kiyaye.
Tana isa mijin bai dawo ba sai dare, ya dawo ya sameta, Yace. '' Kin dawone? Tace. Eeh! Yace yayi kyeu. Washe gari zai fita, tace. '' Mai gida baka bada kudin cefane ba, sai yace kunu za'ayi. Kawai sai ta fashe da kuka, tayita bashi hakuri cewa tayi kuskure kuma bazata karaba...
Hhhhh