WAƊANDA MALA'IKU SUKE YIWA SALATI



WAƊANDA MALA'IKU SUKE YIWA SALATI:

Allah Ya Bamu Labari Acikin Alqur'ani Mai Giram, Lallai Mala'ikunsa Suna Yin Salati Ga Annabi S.A.W. Allah Yana Cewa: {Lallai Allah Da Mala'ikunsa Suna Yin Salati Ga Annabi"S.A.W" Yaku Wadanda Sukayi Imani Kuyi Salati Agareshi.....}. 
 Suratul Ahzab. 

Kuma Allah Yana Bamu Labari Cewa Mala'iku Suna Yin Salati Ga Mumminai. Allah Yana Cewa:
{Allah Shine Yakeyin Salati Agareku,Da Kuma Mala'ikunsa, Dan Yafitar Daga Duffai Zuwa Ga Haske}. 

MA'ANAR SALATIN MALA'IKU:
Salatin Mala'iku Ga Mutane Yana Nufin Nema Masu Gafara Da Yimasu Addua Awajan Allah. 
 ﻈﺮ : ﻓﻀﻞ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻋﻠﻰ
ﺍﻟﻨﺒﻲ [ 1 / 79 ].     

Annabi S.A.W Ya Bayyana Mana Wadansu Mutane Da Allah Ya Sanya Mala'iku Suyi Masu Salati,Ga Kadai Daga Cikinsu:

1-DUBA MARAR LAFIA:
Annabi S.A.W Yana Cewa: [Babu Wani Musulmi Da Zai Je Duba Marar Lafiya Musulmi, Face Sai Allah Ya Aiko Masa Mala'iku Guda 70,000 Suna Yi Masa Salati Akowane Lokacin Na Yini Yaje Dubasa, Har Sai Yakai Yammaci,Idan Kuma Da Dare Har Sai Sunkai Safiya]. 
 ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ ﻭﺍﻟﺘﺮﻫﻴﺐ [ 3/197

2-WADANDA SUKE YIWA ANNABI S.A.W SALATI:
Annabi S.A.W Yana Cewa: [Babu Wani Bawa Da Zaiyi Salati Agareni,Face Mala'iku Sunyi Masa Salati, Matuqar Yayi Mani Salati,Sai Bawa Ya Yawaita Yi Mani Salati Ko Ya Takaita]. 
 ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ
[ 5/174 

3-MASU YIN SAHUR:
Annabi S.A.W Yana Cewa: [Lallai Allah Da Mala'ikunsa Sunayin Salati Ga Masu Shan Sahur]. 
 ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ ﻭﺍﻟﺘﺮﻫﻴﺐ [ 1 257/
 ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ ﻭﺍﻟﺘﺮﻫﻴﺐ
[ 1/258 

4-MASU KOYAR DA MUTANE ALKHAAIRI:
Manzon Allah S.A.W Yana Cewa: [Lallai Allah Da Mala'ikunsa Da Ma'abuta Cikin Sama Da Kasa,Hatta Tururuwa Acikin Gidanta Da Kifi Acikin Ruwa Sunayin Salati Ga Wadanda Suke Koyar Da Mutane Alkhairi]. 
 ﻭﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ
ﻭﺍﻟﺘﺮﻫﻴﺐ [ 1 / 19.      

5-MASU CIKE SAHUN SALLAH:
Annabi S.A.W Yana Cewa: [Lallai Allah Da Mala'ikunsa Sunayin Salati Ga Masu Sadar Da Sahu]. 
 ﻣﺸﻜﺎﺓ
ﺍﻟﻤﺼﺎﺑﻴﺢ [ 1 / 241 
Abinda Ake Nufi Da Sadar. Da Sahu:Shine Mutum Yaga Wani Gurbi Asahun Gabansa Sai Ya Matsa Ya Sadar Da Shi Yacikesa. 

6-WADANDA SUKE YIN SALLAH A SAHUN FARKO:

Manzon Allah S.A.W Yana Cewa: [Lallai Allah Da Mala'ikunsa Suna Yin Salati Ga Masu Yin Sallar A Sahun Farko.......]v 
 ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ ﻭﺍﻟﺘﺮﻫﻴﺐ [ 1 / 58 


 ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ ﻭﺍﻟﺘﺮﻫﻴﺐ
[ 1 118/ 

7-MASU JIRAN SALLAR BAYAN SALLAH ACIKIN MASALLACI:

Annabi S.A.W Yana Cewa: [............Kuma Mala'iku Suna Yi Masu Salati Matukar Dai Suna Cikin Innda Sukayi Sallah, Suna Cewa: Allah Kayi Masa Gafara Allah Kayi Masa Rahama, Allah Ka Karbi Tubansa, Sunayi Masa Hakan Matukar Baiyi Hadasi Ba].  
 ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ [ 1 / 728

ALLAH KA SANYA MU CIKIN BAYINKA WAƊANDA KAKE YIWA SALLATI DA MALA'IKUNKA

 
Post a Comment (0)