Ina Son Karin Bayani A Kan Sallar Walha?
TAMBAYA❓
;
Asalamu Alaikum malam ya aiki malam, don Allah ya ka’idar sallar walaha take? Allah ya saka da Alheri.
:
AMSA👇
:
Wa’alaykumussalam, To ‘yar’uwa sallar walaha ba ta da wani adadin raka’o’i na musamman, Za ki iya yın raka’a biyu ko hudu ko shida da sallama uku, mafi yawan abin da aka rawaito daga Annabi s.a.w. a sallar walaha shi ne raka’a takwas, kamar yadda ya yi ranar bude Makka, Bukhari ya ambaci kissar a hadisi mai lamba ta: 5806. Lokacin sallar walaha yana farawa daga sanda rana ta fara zafi, kamar yadda hadisin Muslim mai lamba ta: 748 ya tabbatar da hakan, har zuwa dab da karkatar rana daga tsakiyar sama.
Allah ne mafi sani.
Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.