BOYE KAYA DON JIRAN TSADARSA
Tambaya
Shin malam mutum zai iya ajiye wake, ko dawa ko masara zuwa lokacin da sukayi tsada sai ya sayar da su?
Amsa:---
1) Sayan kaya a 'boye da nufin sayarwa a tsadarsa haram ne, shi ne "Al-Ihtikar".
[SAHI'HU MUSLIM; 1605, SILSILATUS SAHI'HA; 3364]
2) Halatta boye wani abinci banda wani, bai inganta ba. Boye kowane abin sayarwa haram ne.
[AL-MUDAWWANA; 4/291]
3) Babu laifi idan a wani gari ne za a saya a kai wani gari.
[MAWA'HIBUL JALIL; 4/227, AL-MUGNY; 4/154]
4) Babu laifi idan manomi ne ya boye amfaninsa wanda ya noma.
[AL-QAWA'NI'NUL FIQHIYYA; 169]
5) Babu laifi idan a lokacin arahar kaya ne a ka saya a ka boye.
[AL-MUNTAQA; 5/16, NAYLUL AWTAR; 5/278]
6) Babu laifi idan a lokacin sayansa mutane ba su shiga damuwa ba, ko da ya na tsada.
[AL-BAYANU WAT-TAHSIL 17/284]
7) Babu laifi idan an boye ne domin bukatar iyali. Annabi ya kan adana ma iyalansa abincin shekara.
[SAHI'HUL BUKHA'RY; 2904]
Amsawa:-- Sheikh Abdurrazaq Yahya Haifan
.30/01/2022
.
Domin samun fatawoyin Malam Kai tsaye sai a bibiye mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram:---- https://t.me/Miftahulilm2
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248