DUK LOKACIN DA AKA SAMU CUTA A ZAMANTAKEWAR AURE, SAKI YA HALATTA !

DUK LOKACIN DA AKA SAMU CUTA A ZAMANTAKEWAR AURE, SAKI YA HALATTA !


Tambaya
Assalamu alaikum malam Shin yana halatta macce ta cigaba da zama da mijin dake neman mata, kuma har cikin gidanta yake kawo matan banzar, idan ta fita unguwa?

Amsa
Wa alaikum assalam, Ayi masa Nasiha, in bai ji ba, za ta iya neman rabuwa da shi, saboda Allah ya shar'anta saki ne saboda tunkude cuta daga Ma'aurata ko daya daga cikinsu, kamar yadda Allah yake cewa a cikin Suratun Nisa'i:
"وإن يتفرقا يغن الله كلا من سعته"
Wannan halayyar kuma bayan kasancewarta haramun a Musulunci, akwai cutar da abokin zama a cikinta.

Allah ne mafi sani

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

20/01/2020

Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram:---- https://t.me/Miftahulilm2

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)