Kalaman da duk masoyi bai so daga Masoyinsa su ne.
1. A duk lokacin dana dubi fuskar wance sai na ji na afka farin ciki duk da cewa ke ce sarauniyar zuciyata.❌
2. Tabbas wance ta kai maƙura a iya kwalliya ba shakka tana da kyau, amma kin san ke ce masoyiyata .❌
3. Masoyina ina tasan in baka labari wallahi ka yi matuƙar dace da samun aboki domin duk rana sai mun yi chat sama da sau goma a rana, halinku ɗaya da shi don haka nake ƙara sonka.❌
4. Abin ƙaunata ko da yaushe cikin soyayyarka nake dare da rana jin sonka nake yana bin jini da tsoka ya hanani ci ya hanani sha ban ji ban gani, ka turomin wani abu zan shiga kasuwa abin ƙaunata.❌
5. Ina sonka kamar yadda biri ke son ayaba Masoyina ƙaunarka nake kamar yadda mage ke son ƴaƴanta mahaukacin sonka nake kamar yadda mahaukaci ke son bola.❌
6. Ya ke abar ƙauna don Allah ki ban dama na raɓe ki don jin gundarin ƙaunata dake manne a jikinki ko da na mintuna ne.❌
Yawwa kuma kowa ya kawo na shi.🥰😍💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼