LABARIN ALTI DA KUTARE

LABARIN ALTI DA KUTARE


A zamani mai tsaho daya shude anyi wani tsoho mai suna Alti. Alti mutum ne mai girman kai, zafinrai da kuma rigima. Wata rana anyi ruwa an dauke sai ALti yaje kasuwa don yasai takarkari, shigarsa keda wuya sai jakin wani kuturu yai tutsu ya kada wannan kuturu ana atare atare sai Alti ya tunada tsohon tsiminsa, basai ya tari jaki gaba-da-gaba ba. Kai kuma aura (jaki) kana zuwa sai ka kama cunar rigar Alti kai taja kana cizo har tai kaca-kaca. Kuturu na zuwa sai yasa gundulmi garin dukan jaki sai ji kake fas a kan Alti. Alti yai sama ya fado asume, yan sannu-sannu suka lalubeshi tas. Koda Alti ya farfado yaga ba kuturu ba jaki, kuma ba kudi sai ya dinga zagayawa kasuwa in yaga kuturu sai ya tambaya kaine mai jaki, sai ya wuce, hala sai ga wata tsohuwar kuturuwa tai yawo bata samu ko aniniba, koda ya tambayeta sai tace eyeh nice mai jaki. Gogan naku kawai sai ya rufe kuturwa da duka. Koda sauran kyadayen sukaga haka, kawai sai suka rufeshi da duka da mangari... Da kyar aka kwa ceshi. Koda aka nutsa, sai Alti yace shi dai ya hakura amman lallai kuturunnan na farko sai ya nuna mishi gudumar daya dakeshi da ita..hahahhahah kurunkus.
Post a Comment (0)