MACEN DA BA A IYA SAKI: GABATARWA

*MACEN DA BA'A IYA SAKI............* 

🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕

           *GABATARWA*

   Dukkan yabo da kira ri sun tabbata ga Allah subhanahu wata'ala tsira da amincin ubangiji su tabbata ga farin jakada babba dan Abdullah Muhammadurrasulullahi (saw) da iyalansa da sahabbansa fararen jakadu "yan mazan jiya baki daya. 
    Bayan haka haqiqa akwai wasu dabi'u da halaye da siffofi wadanda babu yadda za'ayi mace tagari ta siffanta dasu face ta kasance abar qauna da bege a wajan mai gidantaba, kuma kalmar saki sai dai ta jita a wani gidan amma ba cikin gidanta ba, babu wani da namiji da zai yi gangancin rabuwa da matarsa mutuqar ta siffantu da wadannan siffofi sai dai qaddarar ubangiji da babu yadda za'ayi da ita, hakan ne yasa muka bunciko wasu dabi'u da halaye guda sittin *(60)* wanda zamu dunga kawowa 'yar uwa mai daraja su domin ta yi koyi dasu ya yin zama da Abun qaunarta. 
   Muna Roqon ubangijin al'arshi ya bamu dama da ikon sauke wannan nauyi cikin amincinsa, kuma yasa munayi ne domin neman yardarsa ya hayyu ya qayyum, muna kira ga malumammu da 'yan uwanmu daliban ilimi kamar yadda ake mana ako da yaushe da zarar anga munyi wani kuskure ayi saurin riskar damu shi domin muma muyi saurin riskarsa, kuma in sha Allah zamu kasance masu karba hannu biyu-biyu muna kowa da kowa fatan Alkhairi. 

Wannan Rubutu zai dunga zuwa kamar yadda sauran rubututtukammu suke zuwa kadan-kadan har zuwa siffa ta qarshe.

*FATAN ALKHAIRI GA MA'AURATA*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*MU HADU A FUTOWA TA 01*

*Rubutawa... ✍️✍️✍️*
*Dalibi mai neman ilimi*
*Nazifi Yakubu Abubakar*
         *(Abu Rumaisa)*
       🥏08145437040🥏

Post a Comment (0)