MACEN DA BA A IYA SAKI 06


*MACEN DA BA'A IYA SAKI............* 

🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕

         *FUTOWA TA 👇*
                  *(06)*
                   

           *MURMUSHI*

   Ya "yar uwa ta mai daraja shin ko kin san cewa murmushi wata ala ma ce da take nuna qauna, soyayya, taushi da rahma? 
   Don haka "yar uwa mai albarka ki sanya murmushi ako da yaushe akan labbanki domin abun qaunarki ya gani aduk lokacin da ida nuwansa suka kai zuwa gareki.
    Kada ki raina aikata hakan domin tabbas aikata hakan zai janyo miki abubuwa guda biyu na farko samun lada wajan mahaliccinki, saboda farin jakada babba dan Abdullah Muhammadurrasulullah saw yana cewa "kada ka raina kyakykyawan aiki duk kankantansa, ko da ka hadu da dan uwanka da sakakkiyar fuska ". 
  Haka ya qara cewa "murmushinka a fuskar dan uwanka kana da ladan sadaka ". 
   Na biyu qara samun qauna da soyayya daga wajan mai gidanki, an tambayi wani miji shin wai wane abu ne yake saka ka jin da di da annu shuwa daga wajan matarka? Sai yace duk lokacin da na kalli fuskar mata ta tana cike da murmushi tare da walwali. 
  Aka tambayi wani kaifa sai yace "dukkanin wata wahala da na shawo tana gushewa ya yin da mata ta abar qaunata take tara ta cikin murmushi.
   Sai aka qara tambayar wani shi kuma sai yace "ai murmushin da mace za ta yiwa mijinta acikin gida shine rabin jin dadin rayuwar Auratayyya, daya rabin kuma yana cikin hutawar da zai samu acikin gida.
    Ya "yar uwa mai daraja kalli yadda wadannan mazaje ke baiyana halin da suke tsintar kansu ya yin da suke fuskartar fuskokin matansu cikin murmushi, haka zalika kema idan zaki dunga aikata hakan haka mai gidanki zai dunga ji, ki sani ya "yar uwa mai Albarka murmushinki zuwa ga abun qaunarki na daya daga cikin mafi girman makami da zakiyi amfani dashi wajan mallakar zuciyar abun begenki, kuma tabbas aikata hakan zaki kasance cikin daya daga cikin matan da muke wa laqabi da macen da ba'a iya saki.


*FATAN ALKHAIRI GA MA'AURATA*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*MU HADU A FUTOWA TA 07*

*Rubutawa... ✍️✍️✍️*
*Dalibi mai neman ilimi*
*Nazifi Yakubu Abubakar*
         *(Abu Rumaisa)*
       🥏08145437040🥏
Post a Comment (0)