MACEN DA BA A IYA SAKI 07

*MACEN DA BA'A IYA SAKI............* 

🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕

         *FUTOWA TA 👇*
                  *(07)*
                   
      *LADABI WAJAN MAGANA*

    Da yawa daga cikin mata suna yin kuskure ya yin da suke yin magana da mazajen su, basa zabar kyawawan lafazi masu ratsa zuciya lokacin hirar su hakan na jawo rashin jituwa tsakanin ma'aurata. 
   Don haka "yar uwa mai daraja kiyi kokari wajan zabar kyawawan lafazi ya yin magana da mai gidan ki ta hanyar ladabi da taushi hadi da nutsuwa,kalaman ki su Kasance ako da yaushe tare da girmamawa da mutun ta wa, ki guji kausasa harshenki da nuni da dan ya tsa zuwa ga mai gidanki haka zalika ki guji Amfani da kalmomi masu ciwo ya yin hira dashi. 
  Matar sa'id bn musayyab tana cewa "bama magana da mazajen mu sai dai kamar yadda kuke magana da sarakunanku :Ranka ya dade, Allah ya qara maka lafiya". 
   Ya ke "yar uwa ya kasance kina da kyawawan lafazai ya yin kiran mijinki ko amsa buqatar sa kamar "Ranka ya dade, baban wane, abun qaunata, mai martaba, malam,Dr, prof, yayana da sauransu, kuma acikin suna yen da zakiyi amfani dashi ki kula sosai ki ga wanne daga cikin su yafi qauna sai ki lazimce shi. 
  Haka zalika Asma'u bnt kharija tana yiwa "yarta nasiha ya yin da zata aurar da ita "kada ki bari mijinki ya ji wani abu tare dake face daddada". 
  Haka zalika wata mata tana yiwa "yarta nasiha ya yin auran ta tace " ya ke "yata ki lazimci ladabi ya yin magana da mijinki, ki zama baiwar sa zai zame miki bawa, idan kika san maganar da zakiyi babu Alkhairi cikin ta shiru shi yafi ". 
   Wani Matashi yake cewa ban taba ganin wani mutun yana san matarsa ba kamar yadda babana yake san Mahaifiya ta, da aka tambayi baban sai yace ta ya ya bazan qaunace taba, na kasance tare da ita tsawan shekara talatin bata taba daga muryarta ba agabana, bata taba saba umarni na ba.
  Haka zalika "yar uwata mai daraja zaki Kasance tare da abun qaunar tabbas kika lazimci ladabin magana tare da mai gidan ki tabbas kece wacce nakewa laqabi da macen da ba'a iya saka. 

*FATAN ALKHAIRI GA MA'AURATA*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*MU HADU A FUTOWA TA 08*

*Rubutawa... ✍️✍️✍️*
*Dalibi mai neman ilimi*
*Nazifi Yakubu Abubakar*
         *(Abu Rumaisa)*
       🥏08145437040🥏

Post a Comment (0)