MACEN DA BA A IYA SAKI 08

*MACEN DA BA'A IYA SAKI............* 

🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕

         *FUTOWA TA 👇*
                  *(08)*
                   
*YIN TARAYYA DASHI WAJAN FARIN CIKI DA BAKIN CIKI*

  Ya "yar uwata mai daraja kiyi kokari wajan girmama abun da mijinki yake ji cikin zuciyar sa, kiyi tarayya dashi wajan farin cikin sa da bakin ciki, domin ita rayuwar auratayyah tana jujjuyawa ne tsakanin farin ciki da bakin ciki. 
  Zaki samu kyakykyawan misali wajan ummuna khadija bnt kuwailid Allah ya qara mata yarda yadda mace take tarayya da abun qaunar ta wajan farin cikin sa da bakin ciki sa, haqiqa ummuna khadija tayi rayuwa da farin jakada babba dan Abdullah Muhammadurrasulullahi saw cikin mafi kyawun ranaku tare da farin ciki, ya yin da wahyi ya sauka gare sa ya tsorata yana zuwa wajanta, sai tace cikin sauti mai cike da kwarin gwiwa da tausasawa :"Kalla ubangiji bazai taba wulakanta ka ba, sannan ta gaya masa maganganun da zasu kwantar masa da hankali, daga nan ta ci gaba da taimaka masa cikin yada da'awarsa da dukiyarta da lokacin ta har lokacin da ubangijin al'arshi ya dauki rayuwarta. 
   Haka zalika umama "yar haris tana yiwa "yarta nasiha ya yin da zata kai ta gidan mijinta tace da ita "ya ke "yata ki guji yin farin ciki ya yin da mai gidanki yake cikin bakin ciki, haka zalika da yin bakin ciki ya yin da yake cikin farin ciki, domin aikata hakan na nuni da cewa kin raina sa ko kuma kina bakin ciki da abun da ya same shi". 
   Haka zalika wata mahaifiya tana yiwa "yarta nasiha tace "Nayi Rayuwa tare da mahaifinki tsawon shekara Ashirin da biyar (25)bai taba ganin bakin ciki na ba ya yin da yake farin ciki ko kuma murmushi na ya yin da yake cikin bakin ciki ". 
   ya "yar uwa mai daraja bari na baki wani labari "wani mutum mai tarin dukiya ya auri wata mata mai kyawawan dabi'u sai ya yalwata mata da duk kanin wani abu da mace take buqata acikin gidan mijinta, sai talauci ya same shi duk dukiyarsa ta hallaka ya zama bashi da komai, sai wannan matar tasa ta basa duk kanin wani abu da ta mallaka daga wajan sa da wanda tazo dashi daga gidan babanta zinare ne da komai da komai, ya ci gaba da juya su har ya kara tsayuwa da kafafuwansa karo na biyu, ya mai da mata da duk wani abu da ta basa da makamancinsa rubi biyu, wannan kyauta ce gare ta saboda yadda ta tsaya ajingi ne dashi da kuma gefansa har ya kai inda yake". 
    Ko iya nan na tsaya ya ke "yar uwata mai daraja zaki fahimci cewa tabbas ta rayya da miji ya yin farin cikin sa da bakin ciki sa na iya jawo miki falala mai girma kalli yadda lamarin wannan baiwar Allah ya kasance, mai zai hana ki aitaka hakan domin tsira duniya da lahira, tabbas idan ki ka siffantu da wadannan siffofi sai dai kiji labarin saki amma ba cikin gidan ki ba, domin tabbas kin fi karfin saki.
   
*FATAN ALKHAIRI GA MA'AURATA*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*MU HADU A FUTOWA TA 09*

*Rubutawa... ✍️✍️✍️*
*Dalibi mai neman ilimi*
*Nazifi Yakubu Abubakar*
         *(Abu Rumaisa)*
       🥏08145437040🥏

Post a Comment (0)