*MACEN DA BA'A IYA SAKI............*
🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕
*FUTOWA TA 👇*
*(09)*
*KI TAIMAKAWA MIJINKI WAJAN NEMAN HALAL*
Ya "yar uwa mai daraja shin ko kin san cewa duk kanin wani jiki da ya tsuro da naman haram wutar jahannama ce tafi da cewa da shi, kiyi kokarin taimakawa mijinki wajan neman halal.
Matan magaba ta sun kasance duk lokacin da mazajen su zasu futa gurin aiki suna yi musu nasiha da cewa " ya kai bawan Allah ka guji neman haram, zamu iya rayuwa da yunwa amma baza mu iya haquri da shiga wuta ba, idan ka samu halal ka zo mana dashi duk kankanta sa idan baka samu ba ka dawo gida.
Bari na baki wani labari ya "yar uwata mai Albarka "wata rana wata mata tana tafiya a kasuwa sai ta tsinci wata jaka cike da kudi masu tarin yawa, sai ta dauka tazo gida da ita, sai ta bawa mijinta, labarin abun da ya faru na tsintar wannan jakar, sai yace ai kawai suyi amfani da wannan dukiyar sai ta hana sa, sai tace dole yaje ya yi cigiya yace mun samu amanar dukiya duk wanda ya ba shi labarin jakar da ala momin da yake ciki to tasa ce, haka akai yana zuwa kasuwa ya fara cigiya sai ga wani bawan Allah nan yace jakata ce ina tafiya akan doki ne sai ta fado kuma aciki akwai dinare guda dubu (1000)ya basa duk labarin abun da ke cikin wannan jakar, sai yace masa, mata ta ce ta tainceta a kasuwa, sai wannan mai dukiyar ya yi murmushi sai yace wannan dukiyar sadaka ce na futo ne domin na samu wanda ya can canta da ita na basa, babu wanda ya cancanta da ita face kai da matarka ".
Ya "yar uwata mai daraja ki sani cewa duk lokacin da kika taimaki mijinki wajan hana sa neman haram tabbas ubangijin al'arshi zai baku abun da ya fisa ta hanyar halal, haka zalika zaki so da qauna wajan sa domin ya san cewa tabbas kece matar da tafi da cewa dashi duniyarsa da lahirarsa, shin "yar uwa mai daraja shin irin wannan matar tasan wani abu da ake kira saki kuwa?.
Haka zalika kema da zaki siffantu da irin wannan siffar da kin Kasan ce daya daga cikin matayen da nake wa laqabi da cewa macen da ba'a iya saki.
*FATAN ALKHAIRI GA MA'AURATA*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*MU HADU A FUTOWA TA 10*
*Rubutawa... ✍️✍️✍️*
*Dalibi mai neman ilimi*
*Nazifi Yakubu Abubakar*
*(Abu Rumaisa)*
🥏08145437040🥏