MAGANIN MANTUWA

MAGANIN MANTUWA


TAMBAYA❓
:
Nine ina yawan mantuwa kuma koda karatu aka koya min to malam ana fada to wallahi a wajen nake mantashi nayi nayi naga nacire wannan abun amma nakasa shin ko akwai addu'a da za,atai makamin dashi ne malam na yawan mantuwa Nagode Allah yasaka da alkairi yakuma bada lada Malam
.
AMSA👇
.
Ban san wata addu'a da aka tanadar don magance mantuwa ba, amma akwai matakan da zā ka bi don samun sauki in sha Allah.

— Daga cikin abubuwan da zai taimaka maka wajen magance yawan mantuwa, akwai 'kokarin nisantar zunubai manya da 'kanana, shi ilimi haske ne, Aʟʟαн(ﷻ) bā Ya zaunar da shi a zuciyar mai yawaita sa6a maShi, sai dai idan ba Shi da bukata ga iliminsa.

— Na biyu shi ne yawan yin adhkar, tabbas ambaton Allah na taimaka wa zuciya wajen adana abin da aka haddace. 

— Ka dinga natsuwa tare da mayar da hankali a kan abin da ake koya maka, kada ka yawaita tunanin wasu abubuwan daban, kuma ka dinga 'kokarin bitar karatun da aka yi maka.

— Ka dinga cin abinci masu 'kara lafiyar kwakwalwa, kamar zuma, dabino, da sauran su. 

— Kallon fina-finan batsa da istimna'i suna dakushe kwakwalwa, wajibine a nisance su.

— A dinga kokarin yawaita karatun alqur'ani da bibiyar ma'anoninsa. 

Idan ka yi hakan in sha Allah za ka ga canji na alkhairi.

 Wallahu A'lamu.


Post a Comment (0)