MASU KWAƊAYI

MASU KWAƊAYI 


Wani Babarbare ne da Bafulatani suka fita yawo wajen gari, sai arnan daji suka kama su, suka kai su wajen sarkinsu. Shi kuwa sarkin sai ya nuna masu wani lambu ya ce su shiga su tsinki duk dan itacen da suke so. Bayan wani lokaci sai ga Bafulatani ya fito da manya- manyan mangwarori guda biyu a hannunsa. Nan take sarkin ya ce wa fadawansa su danne shi su saka masa mangwarorin a duburarsa. Nan take suka cika umurni, Bafulatani ya ci bakar wuya. Ya daga kai ke nan sai ya hango Babarbare, ya kuwa kece da dariya. Da aka duba domin a ga abin da yake wa dariya, sai aka ga ashe Babarbare ne ya tsinko manya- manyan kabewa guda biyu a hannunsa yana tahowa wajen sarki.
Post a Comment (0)