SHIN WAJIBINE YIWA JARIRI ASKIN SUNA
TAMBAYA❓
:
Assslam alaika warahamatullah Dr tambaya ta itace don Allah wai wajibi ne yiwa jariri askin suna idan aka haifesa ya cika kwana bakwai ?
:
AMSA👇
:
Wassslam alaiki warahamatullah to yar uwa hadisi sahihi ingantacce yazo Annabi s.a.w. yace idan aka haifi jariri a kawar da najasa da kazantar da take kansa a ranar cika kwana bakwai dinsa
Umarni ne Annabi S.A.W. yayi yace a yiwa yaro aski manzon Allah ya ambaci wannan gashi dake kan jariri da kazanta to kenan domin tabbatar da umarnin Annabi ya zama wajibi a aske kan jariri idan ya cika kwana bakwai da haihuwa kuma Annabi s.a.w. ya fada cewa ayi sadaka da gwargwadon dai dai nauyin gashin jaririn sai a duba ko dubu ɗaya koh dubu biyu yadda ya sawwaka a bada sadaka
Kuma wannan umarnin na Annabi s.a.w duk jaririn da aka haifa yace za'ayiwa domin hadisin bai ware yace banda mace ba yana magana ne akan jariri to kaga kenan jariri namiji da mace duk akwai wannan dattin kazantar a kansu na mahaifa da suka kwanta idan aka katse sa sai lafiyayyen gashi ya fito.
Allah shine mafi sani
Amsawa
Dr. Abdallah Usman Gadan Kaya
Yaku Yan'uwa masu Albarka ku taya mu yaɗa wannan karatu/sako zaku samu lada mai yawa, Amma don girman ALLAH kada ku kwafa ku goge wani abu daga ciki. Kuji tsoron ALLAH