SHIN HAR YANZU KUNA SON JARUMAN BOLLYWOOD SABODA ADDINI?

TUNATARWA: SHIN HAR YANZU KUNA SON JARUMAN BOLLYWOOD SABODA ADDINI?


By ABBA INDIA DALA.


Wannan Ba Bakon Abu Bane Daga Rubuce-Rubuce na Ga Duk Masu Bibiyar Baza Su Manta da Yawan Abinda Nake Rubutawa da Yake da Alaqa Da Jaruman Bollywood Ko Fina-finan su Wasu Lokutan Nakan Tunatarwa ko Wayer da Kan Wadanda Basu Sani ba Idan Na Fahimci Suna Zakal kalewa a Kan Jaruman su Har Su Rinqa Ganinsu Kamar Wasu Waliyyai Saboda Tsananin Soyayyar da Suke Musu Kuma Hakan Ya Samu Asali Daga Yanda Suke Kayatar Dasu Daga Fina-finai ba To Ni a Kullum Burina Shine Mutane Susan Irin Soyayyar da Zasu Yi Musu ( Abinda Nake Nufi Shine Su So Su Iya films Watau Da Angama Kalla An Gama da Babunsu) Domin Kar Mu Zama Cikin Wadanda Ake Tasun Da Wadanda Maqiya Allah ne Ko Suna Yaqar Umarnin Allah Watau Munafikai Har Ila Yau Mu Kalli Film Kawai Domin Nishadi ko Raha.

Kar Na Kai Ga Tsayin Rubutu Banyi Akan Haqiqanin Tunatarwar yau ba Watau Game da HIJAB Sanin Duk Wani Me Bibiyar Kafar Sadarwa ne Yasan Yanda Ake Hantarar Mata Masu Saka Hijab da Suke a Kwalejin Karnataka ta kudancin India Amma Tunatarwar Shine Har Indai Mutum Bazai Damu da Al'amarin Addininsu ba Sama da Neman Duniya Ko Taron Mabiya ba To Be Kamata Ku a Matsayin ku Na Musulmai Masu Kishin Addini Kuyi Tunanin Zaku Kaunace Shi Domin Addini ba, Tabbas Nasan Cewa Duk Da Nasha Tunatarwa Kan Cewa Su Masu Suna Khans Musamman 3khans Suna Fifita Son Daukaka Sama da Muslincinsu Har Ma Wasu Suna Jinginawa Kansu Wani Abu Na Shirka ko Kafirci Saboda Su Masu Wannan Addinin Su Kaunace su To Bazan Gaji Wajen Kara Jan Hankalin ku Kan Cewa Kar Mu Kuskura da Son Jaruman Bollywood Saboda Wai Su Musulmai ne Domin Wasu Sun Sani Wasu Basu Sani ba Kan Kaucewar su Bisa Ga Koyarwar Musulinci Yana da Kyau Mu Kiyaye Mu Kara Sanin Yanda Zamu Dauke Su.
Allah ya tsare Imanin mu.

#AbbaIndiaDala
Post a Comment (0)