SHIN YA WAJABA GA MAZINACI YA KAI KANSA, DON A TSAYAR MASA DA HADDI ?

SHIN YA WAJABA GA MAZINACI YA KAI KANSA, DON A TSAYAR MASA DA HADDI ?


*Tambaya:*

Assalamu alaikum Malam wani Bawan ALLAH ne yake son dan ALLAH a taimaka a amsa masa wannan tambayar:- shin idan mutum ya aikata wani zunubi akan haddi na musulunci, kuma ya tuba, to shin sai ya gabatar da kansa ga shari'a akan wannan haddi na musuluncin ???

*Amsa :*
Wa alaikum assalam To 'yar'uwa idan har hakkin mutane ne, to dole sai ya biya su, kuma tuba ba zai isar masa ba, kamar wanda ya yankewa wani gaba, amma idan hakkin Allah ne, to mutukar ya tuba Allah zai iya karbar tubansa, ko da bai je wajan alkali ba, Annabi s.a.w. yana cewa : "Duk wanda ya zakkewa wani zunubi da yake wajabta haddi, to ya suturta da sitirar Allah, ya tuba zuwa ga Allah, saboda duk wanda ya bayyana hakan gare mu, za mu tsayar masa da haddi" kamar yadda Malik ya rawaito shi a Muwadda'a a hadisi mai lamba ta 1508, Ibnul-mulakkin ya inganta shi a Badrul-munir shafi na : 5275.

Malamai suna cewa : Abin da ya fi ga wanda ya aikata zunubin da yake hakkin Allah ne, kuma ya ke wajabta haddi, ya tuba zuwa ga Allah, ba sai yaje wajan alkali ba. Don ya yanke masa hukunci, saidai Imamul-mawardy yana cewa, idan ya ga alamun Allah bai amshi tubansa ba, to zai fi kyau ya je wajan shugaba, don ya tsarkake shi, saboda tsayar da haddi yana kankare zunubai.

Allah ne mafi sani 

Duba: Alhawy Al-kabiir 13\334, Raudhatu Addalibin : 357.

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

19\2\2015


Domin samun fatawoyin Malam Kai tsaye sai a kasance damu a 

FACEBOOK⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

TELEGRAM⇨
https://t.me/Miftahulilm2

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)