GULMA AJALI!!!

GULMA AJALI!!! 


 

Wani mutun yazo gurin KHALID BN WALEED yace masa Lallai wane (ya fadi sunan wani) yana zagin ka. 
Sai KHALID yace: wannan littafinsa ne, yana da damar ya cikashi da duk abinda yaso. 
 

Wani kuma ya cewa WAHAB BN MUNABBIH Wane yana zagin ka. 
Sai WAHAB yace: Shin yanzu kai Shaidan bai samu wani dan aike ba duk cikin mutane sai kai? 
 

Haka wani mutum yazo gurin wani bawan Allah yace; Wani ya zage ka. 
Sai mutumin yace: Shi ya harbeni da kibiyar da bata same ni ba, kai kuma ka daukota kazo ka daba mini a zuciyata. 
 

Wani mutum yazo gurin Imam SHAFI'I yace; wa ne yana ambatarka da munanan kalamai. 
Sai Imam SHAFI'I yace: idan har da gaske kake toh lallai kai ANNAMIMI NE,
Idan kuma qarya kake toh kai FASIQI NE, saboda haka ka tafi ka bani guri. 
 

NASIHA: Kada ka taÉ“a daukar gulmar wani ka kaiwa wani, 
domin wanzar da qauna da soyayya a cikin al'ummah, 
kabar mutane suyi farin ciki tare da yan uwansu. 
Kai kuma ka guji ANYI-ANCE. 
Allah ka gyara mana dabi'un mu na fili dana boye.
Post a Comment (0)