DUK WANDA YA ZO NEMAN AUREN YARKU, MATUKA KUN YARDA DA ADDININSA DA HALAYYARSA, TO KU AURA MASA.

DUK WANDA YA ZO NEMAN AUREN YARKU, MATUKA KUN YARDA DA ADDININSA DA HALAYYARSA, TO KU AURA MASA. 


https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
:
*TAMBAYA*❓
:
Malam dan allah ko laifine mace tace bata son wani bayan sundade suna SOYAYYA ? Saboda tagano cewa bayada cikakkun halayen islam kamar ilmi cika alqawari kula da sallah dasauransu , kuma minene hukuncin mace yarinya taga wani mutumen kirki ko malami tagayama cewa tana sanshi amma kuma saitake jin kunyar gayamishi .?
:
*AMSA*👇
:
 Amfanin Mu'amalantar Mutum Kafin Aure shine, Ka san Halayensa. Idan har Allah ya Taimakeka ka san Halayenta Masu Kyawun da Marasa Kyawun su ko kuma ya taimakeki kika san halayensa Masu Kyau da marasa kyau dinsu. Sai ki Auna kiga Cewar Zamanki da shi zai yiwu Kuwa? Idan zai yiwu sai a Gwada. Idan kuma ba zai Yiwu ba, sai a Hakura.
 Duk da Cewar Ba Lalle bane. Abinda ya zama Matsala a wajen wani, wani kuma ya zama Matsala a wajen sa.
 Misali. Idan kai kana ganin Rashin sanya Shijabi ga mace, Matsala ne a gare ka. Wani kuma shi baya son ma yaga Matarsa ta sa Shijabi. Kaga shi sai ya Aura, Domin wannan ba matsalar sa Bace.
 Sannan Kuma Shin a Musulunci ma ya Halatta ki Zauna da shi a Matsayin Mijinki.? Ya Zama Uban Yaranki,? Alhalin kuma ke ki Na Musulma?
 Ma'ana Musulunci ya yarda mai irin wadannan halayen ya zama Mijinki a Matsayin Musulma ta Gari? Sai ki Auna Da Ma'auni na Adalci. Ba Son Zuciyarki zaki bi ba.
  A Zahirin Gaskiya kuma a Ma'auni na Musulunci. Ga Mai Irin wadannan Dabi'u da kika Lissafo. Bai Kamata ya zama Mijinki ba.
 Na Farko, Kince Baya Yin Sallah. Wanda akan Sallar nan fa, Musulunci ya Halatta a Raba Auren Wanda baya yin sallah da wadda take yin sallah. Ko da kuwa yana cewa Shi Musulmi ne.
 Duba da Hadisin da Manzon Allah saw yake Cewa. Tsakanin Musulmi da Kafiri, shine barin sallah. Wanda da wannan ne Wasu malaman Suka ce duk wanda baya yin sallah, Kai Tsaye KAFIRI Ne.
 Sannan Kuma ta kowacce Fuska, Musulunci Bai Amince da a dauki diyar Musulmi a Baiwa wanda baya Yin Sallah ba.
 Daya daga Cikin Illar da zaiyi Miki Anan shine, ke Kanki Za'a wayi Gari in har Baki dena wannan sallar ba. Ko kuma ke Kanki Ba zaki damu da yin sallar ba. Domin Shugabanki/Mijinki baya Umartarki da yin ta. Asalima Shi Kansa baya yi. Wanda ya dace ko da zai tafi Masallaci da Asubahi, Ya Tasheki ya ce kiyi sallah.
 Na biyu Shine. 'Yayan da zaki Haifa. Yaya zasu Kasance? Alhalin Mahaifinsu Baya Yin Sallah? Waye zai Umarcesu da Tafiya Masallaci Suyi Sallah? Dole za Suyi koyi ne da Babansu.
  Gashi Kuma Kince bashi da ilimin Addini. Wanda shine Ummul Aba'isin da ya sa ma baya yin wannan sallar. Sabida shi Allah sai ka san shi ne Zaka girmama shi, Sannan kuma Sai Ka San shi ne zaka bauta Masa.
 Gashi Bashi da Cika Alkawari. Alhalin Manzon Allah saw yana Cewa "DUK WANDA BAYA CIKA ALKAWARI, TO BABU ADDINI A GARE SHI".
   Sannan Alkawarin nan za'a Tambayemu Akansa ne a Ranar Alkiyama. Wanda ke Kanki Alkawari Zai dauka Na Cewar, Zai Kula da ke da iliminki da Sauransu. Kinga Kenan, Wanda bashi da Cika Alkairi, ta yaya Za'a Bashi Amana.? Ba zai Kiyaye ba gaskiya.
 Sannan Kince Akwai Halayya na Rashin Kirki, wanda ba ki zayyano su ba. Wanda ko da a Iya nan kika Tsaya. Bai Chanchanta ki Aure shi ba gaskiya.
  Sabida Haka Kenan, Yana da kyau ki bar shi, Ki Hakura da Shi, Komin irin Son da Kike Yimasa. Domin idan baki bar shi ba Sabida soyayya ta Dauke Ki. Za'a wayi Gari wannan son da kike Yimasa , Zai zama Kiyayya.
  Abu na Gaba Shine. babu Kunya sanarwa Mutumin da ka san na Kirki ne cewar kana Son Shi. 
 Wanda hakan ya sha Faruwa tin a zamanin sahabban Manzon Allah saw. Mazan su da matan su. Wanda Wadannan Mutane Sune Mafiya Alkairin Zamani inji Manzon Allah saw.
  Ya taɓa Faruwa kamar yadda Bukhari da Muslin Suka Rawaito, wata Mata ta zo wajen Manzon Allah saw Tace. Tana Son Shi. Ta bashi Kanta ya Aureta. 
 Da wannan ne ma Imamul Bukhari ya Kulla Babi Akan, Cewar BABIN DA YA HALATTA GA MACE TA BAYAR DA KANTA GA MUTUMIN KIRKI DON YA AURETA. Ma'ana ta ce tana son wani Mutumin Kirkin. So irin na Aure. Ba dan wani Abin duniya da yake da shi ba.
Sannan Uwar Muminai, Uwar gidan Manzon Allah Saw, Nana Khadija itace Tace tana son Manzon Allah saw. Sabida Kyawawan Halayensa. Kuma ya Aureta, daga baya Allah ya Sanya Musu Albarka. Wanda bai Taba Haihuwa da wata Mata ba, in banda Nana Khadija. Itace Uwar Yayansa, itace wadda ta Taimaka Masa da Kudinta da Lokacin ta, tin a Farkon Musulunci.
 Sabida haka kenan. Ya Halatta ki sanar da shi ta hanyar ki kira shi a waya ko ki Rubuta a Rubuce ta Massage ki tura Masa ko a Takarda ki Aika Masa ko ta hanyar social median, kamar Whatsapp ko Facebook ko Twitter ko wani social media da sakon ki zai kai gare shi. ko ki Aika wata ta gaya masa kina son Shi ko kuma ke da Kanki ki furta masa ko ki Nuna Masa wata Alama da zai gane hakan. In kin Nuna Masa Zai Fahimta, Sabida Ustazan Nan fa Akwai Fahimta a Wurinsu. Idan da Aure a Tsakanin ku sai kiga hakan ya Zame masa Alkairi, Kema kuma ya Zame miki Alkairi. 
 Domin yana da kyau Mutum ya Auri Matar da take son shi. Ba matar da yake so ba. 
 Idan mace tana son ka. Wallahi zaku Zauna Lafiya. Domin ba zata so Bacin Ranka ba. Amma idan kai ne kake Son ta. Kuma ka sake ta gane hakan. To Wallahi Sai ka banbance Tsakanin Zare da Abawa.
   Sannan Kuma Wallahi Mutumin Kirki Alkairi ne ga Kowacce mace. 
 A Irin Wannan zamanin da Muke Ciki, idan mace ta rasa na Kirki, zata sha Wahala a Rayuwar Auren ta.
 Sayyadina Umar Yace KU BAYAR DA YAYANKU GA MUTANEN KIRKI, IDAN YAYANKU SUNYI MUSU BA DAIDAI BA A GIDAN AURENSU, ZA SUYI HAKURI. IDAN KUMA SUNE SUKA YIWA YAYANKU BA DAIDAI BA. ZASU BASU HAKURI.
 Sannan Kar kiyinTunanin Ae Idan ke ce kika ce kina Son Shi. Zai Iya Wulakanta ki. Yayi miki Gori. Ashe ba Mutumin Kirkin bane. Mutumin Kirki ya san ya Kamata. Baya Wulakanta Mace, sai dai ma Darajarta ta. Sabida ya san Mahimmancinta.
  Wallahi Mata Ina Mai Jan Hankalin ku. Idan kun tashi Aure. Ku Auri Mutanen Kirki. Masu ilimi, masu Addini, masu biyayya da Musulunci, masu biyayya ga halayen manzon Allah saw da Sahabbansa. Nine nan na gaya Muku, Wallahi Zaku Ci Riba.
 Duk wadda ta sake ta dakko Miji domin son Zuciyarta. Zata Fuskanci Matsala.
 Sannan Kuma kar kiyi gaggawar Kawo Namiji a Matsayin Wanda zaki Aura. Ki Jinjina. Aure ba Wasa bane. Kuma Kina yin Addu'a. Indai Irinsu kike Nema. Allah zai kawo Miki irinsa.
 Duk Irin Namijin da Mace take Nema. Shi Allah yake kawo Mata.
 Manzon Allah saw yace. DUK WANDA YA ZO NEMAN AUREN YARKU. MATUKA KUN YARDA DA ADDININSA DA HALAYYARSA. TO KU AURA MASA. IDAN BA HAKA BA. ZAKU HADU DA FITINA.
 Fitina Shine, Idan kin Auri Mutum dan kudinsa. Sai Allah ya Jarrabeki daga baya kudin ya kare a Daidai lokacin da kuma kin hayayyafa da shi. Ba inda zaki je, a haka zaki Zauna a cikin Talaucin. Shikenan sai Tsufa ya Lullubeki. Ga tension na Talauci ga tention na yara.
 Idan kuma kin Aure Namiji ne dan wani Abu. To fa wallahi wannan Abin ba zaki samu ba. Domin sai Allah ya Saukar miki da jarrabawa Akan Wannan Abin da kika Kwallafa Ranki a Kai. Haka Al'amarin Allah yake. Duk abinda Akayi ba dan Allah ba. Sai an Hadu da Fushinsa. Indau har Shine yayi Umarni da wannan Abin.
  Sabida Haka Kenan Kawai Ki sanar da shi cewar kina SON shi. Indai na Kirki ne, sai kiga Allah ya sanya Albarka a Cikin Aurenki.
 Mata da yawa Suna Cewa Allah ya basu Miji Na Gari. Amma kuma Ma'anar Addu'ar ba haka take a wurinsu ba. Da yawa Idan Suka ce Miji na Gari. Akasarin su, MAI KUƊI Suke Nufi.

Allah Shine Masani.

✍️
ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08137783797

GROUP ADMIN:👇
Mal. Khamis Yusuf
+2348087788208
+2348054836621

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)