HIKIMOMIN DA AZUMI YA ƘUNSA

HIKIMOMIN DA AZUMI YA ƘUNSA
-


-
Azumi ginshiƙi ne daga cikin turakun musulunci waɗanda addinin musulunci ba zai cika ba sai da su, Allah da Manzon sa sunyi umarni dashi saboda wasu muhimman manufofi, ga wasu daga ciki:

1. Samun tsoron Allah, saboda mai azumi yana barin abinda yake so saboda Allah, hakan zai sa ya ƙara samun tsoron Allah.

2. Samun kariya daga shaiɗan saboda azumi yana takure hanyoyin shaiɗan wannan yasa zunubai suke ƙaranci a ramadhan.

3. Tuna talakawa da wahalar da suke ciki, saboda duk lokacin da mai kuɗi ya ɗanɗana yunwa zai tuna halin da talakawa suke ciki.

4. Sabawa rai wajen barin abinda take so da kuma haƙuri akan abinda take sha'awa.

5. Kankare zunubai da kuma samun ɗaukakar daraja saboda azumi yana gyara zuciya da kuma rai.

6. Samun lafiyar jiki, saboda azumi yana kariya daga cututtuka masu yawa kamar yadda likitoci suka tabbatar da hakan.

7. Ta hanyar azumi mutum zai saba da yin aiki don Allah saboda azumi sirri ne tsakanin Allah da bawansa.


```Zulaihat Muhammad Umm Adnan```
26/Sha'aban/1443
29/March/2022
Post a Comment (0)