By ABBA INDIA DALA.
Wannan Sharhi Yana da Matukar Muhimmanci ga Duk Wani Masoyin Kallon Fina-Finan India Domin Wannan Abu ne da Kowa Yake Bukatar Sani Kuma Nayi Wannan Sharhi ne Saboda Wayar Mana da Kai Akan Wani Abu da Yake Shige Mana Duhu Kamar Yanda Ni Kaina Tun Bayan Da Wannan Film ya Fito Yake Kasuwa Me Kyau Nakeso Na Kalla Naga Mene Yake Faruwa Aciki Kuma Shin Su Waye Suke Kallonsa Kuma Menene Dalili Kuma Mutane Da Dama Sun Bukaci Na Kalla Nayi Sharhi Saboda Yaqini da Suke Akan Zan Kwatanta Adalci Wajen Sharhinsa To Wannan Dalilin Yasa Wannan Sharhi da Nayi Kamar Sauran Fina-Finan da Nasaba Shekarun Baya ne ba Saboda Nima Na Kara Fadada Tunani na.
Wannan Ya Kara Min Haske Sosai Kuma Da Yawan Musulmai Zasuyi Mamaki da Farin Ciki Yayin da Zance Kusan Kullum Gaskiya Kara Bayyana Take Kuma Duk Yanda Aka Kai Ga Kin Addinin Allah Wata Ran Sai Gaskiya Ta Bayyana Saboda Su Da Yawan Fina-finansu Suna Nuna Musulmi Dan Ta'adda ne Kuma Dan Addinin Hindu Me Gaskiya ne To Amma Wannan Karan Tunaninsu Ya Fara Kwabcewa Kuma Duk Iko ne Na Allah.
Domin Kuwa Duk Wanda Yasan KASHMIR DA JAMMU to Yanki ne da Hadaka da India da Pakistan Kuma Kowa Yasan Cewa Musulmai Sune Suke da Rinjaye Domin Sun Ninka Yan Addinin Hindu To Duk Wani Dalibin Ilimi Na Addinin Muslinci Yasan Cewa Idan Ya Shiga Littafai da Suke Magana Akan Jihadi ( Khitabul Jihad) To Zai ga Cewa Akwai Lokacin da Musulmai Suke da Iko na Shari'a da ta Qa'idance Musu Shine Baza Suyi Gaggawar Yaqar Suba Amma Zasu Kafa Musu Sharruda Idan Sun Rinjaye Su Shine Zasu Hanasu Siyan Makaman dasu Iya Cutar da Musulmai, Zasu Hanasu Shigowa Sansanin su da Sunan Bautawa Gumaka, Zasu Hanasu Daga Murya Har Sujiyo Sautin na Bauta, Zasu Hanasu Buga Kararrawa ta Bauta, Zasu Hanasu Siyan Bayi da Hawa dawakan Alfarma Sannan Duk Wanda Ya Fito da Irin Bautarsu ta Gumaka Ko da Shan Giya Zasu Ladaftar Dashi Sannan Su Watsar da Abubuwan da Suke Bautawa Kuma Duk Kafin Wannan Se An Dora Musu Haraji Har Indai Suka Watsar da Wadannan Qa'idojin Za A Yakesu Domin Kuwa Zasu Iya Kawo Fitina Cikin Addinin Islama.
Amma Kuma Su Yan Hindu Suna So Kowane Lokaci Su Zama Sune Sarakuna a Kowane Yankin Har Su Juya Musulman Kuma Suna Nuna Cewa Kawai Kisa Muslmai Suka Iya Sedai Kuma Acikin Wannan Film Sun Nuna Cewa Su Ma Muslman Suna Kira a Musulta Ko a Fice Daga Yankinsu Ko Kuma Su Kashe Mutum Kuma Suna Nuna Cewa Suma Zasu Fito Suyi ta Tallata Addinin Hindunsu Kamar Yanda Aka Nuna, Sedai a Fahimtata Dole Zasu Gyara Labarin Wajen Suga Cewa Sam Sam Musulmai Basu da Gaskiya Ko Kadan.
GA SHARHIN:
Wannan Film Ya Hada Jarumai Kamar Haka:-
Mithun Chakraborty a matsayin IAS Brahma Dutt,
Anupam Kher a matsayin Pushkar Nath Pandit Sune Fitattu Aciki Kuma Shi Pushkar Shi Aka Nuna Akan Ba Ta Yanda Za Ayi Ya Boye Bautar Gumakan su Domin Shima Yankinsa ne dashi Da Iyalansa Kuma Wannan Dalilin Yasa Aka Afka Musu Aka Kashe Dansa Karan da Jikansa Shiva Amma Karamin Jikansa Krishna Shine Ya Girma Har Takai Yana Can Yana Karatu Ya Samu Labarin Rasuwar Kakansa Pushkar Inda Ya Dauko Tokarsa Ya Nufo da Ita Yankinsu na Kashmir Ya Samu Abokan Kakansa Su Hudu Aciki Akwai Shi Mithun Se Kuma Sauran Sune Punit Issar da Parakash Belwadi da Kuma Bhasha Sumbli Bayan Ya Iso Wajensu da Tukunyar Tokar Kakansa Duk Suka Mike Se Krishna Yace Ya Kuka Tsorata Su Kuma Suka Bashi Amsa Da Cewa Ba Ganinsa Ne Yasa Suka Tsorata ba Kawai Ganin Tukunyar Hannunsa ne Se Shi Kuma a lokacin a wannan Wajen Ya Nuna Cewa Ko Mutuwar Mahafinsa da Yayansa ma Duk Hadari ne A Takaice Tun A Wajen Abokan Kakansa Sun Tabbar Wannnan Yaran Yana Cikin Duhu Be San Kome ba Har Takai Daga Karshe Yaje Ya Gana da Wanda Ya Fito a Dan Ta'addan Watau
Chinmay Mandlekar da ya fito da Suna Farooq Malik Bitta Inda Har Shima Ya Kara Raina Tunaninsa Yace Kaga Duk Abinda Mutane Suke Fada Game Dani Cewa Ni Ina Kisa Duk Karya ne Su Kansu Mahaifinka da Yayanka Bani Na Kashe Su ba Kuma a Take Ya Yarda Ya Dawo Gida Ya Samu Mithun Watau Brahma ya Tambayeshi Ka Gamu Dashi Kuma Yaya Kaganshi Yace Na Ganshi Tabbas Aboki ne Ga Kowa. A wannan lokacin Mithun Ya Zare Ida da Mamaki Yake Cewa Ta Yaya Maqiyi kuma Makashin Mahaifanka Zai Zama Aboki Nan Take Ya Bashi Fayal(Files) Duk Aciki Zakaga Kome Nan Take Ya Fara Karanta The Kashmir files Kuma Ya Tabbatar da Cewa Chinmay Mandlekar da ya fito da Suna Farooq Malik Bitta Shine Yayi Wannan Aika Aikar Amma Kuma Yayi Masa Karya Kusan Zan Iya Cewa a Haka Wannan Film Ya Kare.
Wannan Abu Sunce Ya Faru a Shekara 1990 Amma Ta Yanda Zakusan Gaskiya Shine Tayaya Wadanda Sukayi Kashe-Kashen Nan Zasu Rinqa Karyatawa Kamar Yanda Shi Bitta ya Fadawa Krishna? Duk da Su Da Kansu Suka Tsara Labarin Suka Nunawa Duniya Amma Sun Gaza Wajen Tabbatar da Nuna Cewa Karshen Wannan Azzalumin Beyi Kyau ba Sun Nuna Cewa Yayi Abinda Ya Inganta Zamansu Na Yankin Kashmir da Jammu.
#AbbaIndiaDala