219 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU
HUKUNCIN KARANTA BASMALA A SALLAH?
TAMBAYA:
Assalamu alaikum, ya matsayin karanta basmala a cikin sallah shin ya halatta ko a'a?
AMSA:
Wa'alaikumus salam, Sunnah tabbatacciya ta tabbatar cewa Annabi ﷺ yana karanta 'Bismillah' a cikin sallah kafin karatun Fatiha, kuma yana karanta ta kafin karatun farkon sura, amma banda suratut Tauba, Sai dai duk da haka ba ya karanta Bismillah ɗin a bayyane ko da a sallar da ake karatu a bayyane ne.
Duba Fataáwal Lajnatid Dá'ima (6/380).
Kuma karanta 'Bismillah' kafin karatun Fatiha da sura a kowace raka'a lamari ne da Shari'a ta aminta da shi, in banda Suratu Bará'a. Dubi Fataawal Lajnatid Dá'ima (6/380).
Don haka karanta Basmala a cikin sallah halas ne, wasu malaman ma suna fahimtarsa a matsayin wajibi, wasu kuma akasin haka, maganar halasci ko akwai ta, amma maganar wajabci ko akasinsa nan kam malamai sun yi saɓani.
Allah S.W.T ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
18/09/2019 M.
Daga:
ZAUREN SAQON ANNABTA NA MATA ZALLA