HUKUNCIN SADUWA DA MAI HAILA, BAYAN DAUKEWAR JININ, KAFIN TAYI WANKA

HUKUNCIN SADUWA DA MAI HAILA, BAYAN DAUKEWAR JININ, KAFIN TAYI WANKA


TAMBAYA❓
:
Assalamu alaikum, Malam kasancewar saduwa cikin haila laifi ne, to ina hukuncin saduwa bayan tabbatar da daukewar jinin amma gabanin wankan tsarki??
:
AMSA👇
:
Wa'alaikum assalam, Maganar mafi yawan malamai shine: ba'a saduwa da mai Haila sai ta yi wanka, saboda faÉ—in Allah madaukakin sarki a cikin suratul Bakara aya ta: 222 (Idan Mata suka yi tsarki, to ku zo musu ta inda Allah ya umarce ku), inda suka fassara tsarki a wannan ayar da wanka, Kamar yadda Ibnu Rushd ya ambata a littafinsa Bidayatul Mujtahid.
Saidai shehin malami Abu-hanifah ya fahimci tsarki a wannan ayar da yankewar Jinin haila, wannan yasa suka halatta saduwa da macen da ta kammala haila kafin ta yi wanka. Duk da cewa duka maganganu biyun suna iya shiga ayar, saidai zance mafi inganci Shi ne maganar farko saboda Allah ya kira haila da kazanta a cikin Alqur'ani, kazanta kuma tana bukatar tsafta da gyaran jiki, don kaucewa bacteriar (kwayar cuta) da ta kunsa.

Allah ne mafi sani.

Amsawa:- Dr. Jamilu Zarewa

Yaku Yan'uwa masu Albarka ku taya mu yaÉ—a wannan karatu/sako zaku samu lada mai yawa, _Amma don girman ALLAH kada ku kwafa ku goge wani abu daga ciki. Kuji tsoron ALLAH


Post a Comment (0)